Sanusi II Ya Ci Taro Cikin Kayan Sarauta Ana Tsakiyar Maganar Duba Lamarin Tsige Shi

Sanusi II Ya Ci Taro Cikin Kayan Sarauta Ana Tsakiyar Maganar Duba Lamarin Tsige Shi

  • Muhammadu Sanusi II shi ne babban bako na musamman a liyafar Herbert Wigwe a garin Legas
  • A irin haka Sarkin Kano na 14 ya yi bikin Sallah a jihar Kaduna kamar yadda ya saba tun a 2020
  • Sanusi ya yi fita a kayan sarauta yayin da ake ta surutu a kan yiwuwar komawarsa mulki

Kano - A daidai lokacin da ake surutu game da yadda aka tunbuke Muhammadu Sanusi II daga sarautar Kano, shigarsa ta kara jawo abin magana.

A rahoton Daily Trust, an ji Malam Muhammadu Sanusi II ya halarci wata liyafa da Shugaban bankin Access bank PLC, Herbert Wigwe ya shirya.

Sanusi II shi ne bako na musamman a liyafar da Cif Herbert Wigwe ya shirya a garin Legas.

Wannan ne karon farko da aka ga Sarkin Kano na 14 a fili bayan an ji Rabiu Musa Kwankwaso ya ce gwamnatin NNPP za ta duba abin da ya faru.

Kara karanta wannan

Masarauta: Kwankwaso ya fadi abin da Abba Gida-Gida zai yi kan kujerar sarkin Kano Sanusi II

Kwankwaso ya tada kura

A wata hira da aka yi da shi, Rabiu Musa Kwankwaso ya nuna idan Abba Kabir Yusuf ya hau mulki, zai yi bincike a kan batun masarautar jihar Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan lamari ya jawo hayaniya musamman a shafukan sada zumunta tsakanin magoya baya da masu nazarin gidan sarauta a Arewacin Najeriya.

Sanusi II a Legas
Muhammadu Sanusi II a Legas Hoto: @MSII_dynasty
Asali: Twitter

Tarihin sarautar Sanusi II

A Gwamnatin Kwankwaso ne aka nada Sanusi Lamido Sanusi a matsayin Sarki, ‘yan makonni kadan bayan dakatar da shi daga Gwaman bankin CBN.

Bayan Abdullahi Umar Ganduje ya gaji mulki, sabani ya shiga tsakanin Mai martaba Muhammadu Sanusi II, har ta kai ya tsige Sarkin a Maris na 2020.

Shekaru uku da yin haka, jama’a sun fara ganin yiwuwar a dawo da Sanusi II kan karagar mulki, hakan zai iya jawo a sauke Mai martaba Sarki mai-ci.

Kara karanta wannan

Gwamnati Ta Tsaida Ranakun Bude Titunan Kano-Zaria-Kaduna, Legas-Ibadan, da Gadar Neja

Abin da mutane ke cewa

"Ganduje ya cirewa SLS rawani kuma babu abin da mu ka iya. Soyayyarmu ga SLS ba ta iya taimaka masa da komai ba.
Idan Abba ya ga damar maido shi mulki, babu abin da zai yi. Kiyayyarku ga RMK da Abba ba za ta taimake ku ba.
Abin da kurum za ku iya shi ne ku yi ta surutu a Twitter."

- Mahmud Galadanci

"Ba dai Sanusi Lamido ba ne? Ga Kwankwaso nan, ga Abba, ga Sanusi Lamido dinnan. Sanusi da bakinsa kuma?
Wallahi mutane za su fahimci Ganduje ya yi matukar hakuri da Mai martaba Sanusi II."

- S. Bala

Ana shirin lalata masarautar Kano, ‘yan siyasa za su maida ta abin wasa. Martaba da darajar karagar nan ta fi karfin a rika jagwalgwala ta irin haka.

- Jibreel Khalil

A wani dogon rubutu da ya yi, a karshe Rayyan Tilde ya roki Ubangiji Allah (SWT) ya yi wa mutanen Kano da Mai martaba Sanusi II zabi na kwarai.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya Ta Kashe Naira Miliyan 560 Wajen Ceto ‘Yan Najeriya a Kasar Sudan

Farin jinin Sanusi II

A farkon shekarar nan aka ji labari Muhammadu Sanusi II ya ziyarci Kano, magoya baya kamar su lashe Mai martaba, Sarkin da aka tunbuke a 2020.

Sanusi II ya ce jirginsa ba zai iya zuwa Jigawa kai-tsaye ba, sai ya ratsa ta Kano, hakan ya jawo daruruwan mutane suka duro domin ganin Khalifa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel