Sarkin Kano Muhammad Sanusi Ii
Sarki Muhammadu Sanusi II zai jagoranci hawan babban daki a jihar Kano bayan dawowa daga London. Hakan na zuwa ne bayan sarki Aminu Ado ya tafi Kaduna.
Ana zargin wani matukin tirela da wurgo wani dan Karota da ya shiga motar shi domi duba takardun kayan da ya dauko. Lamarin ya faru wajen gadar Muhammadu Buhari.
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya kai ziyara ga tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar a birnin London ranar Asabar 19 ga Afrilun 2025.
Dan daba da aka fi sani da Abba Dujal ya mika wuya ga 'yan sandan jihar Kano. Dujal ya ce ya kashe mutane a Kano da Jigawa, ya sace babura da wayoyin jama'a.
Bayan rasuwar Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi, manyan yan siyasa da sarakunan gargajiya sun ziyarci fadar Aminu Ado Bayero maimakon fadar Sarki Sanusi II.
Wata Kungiya ta fusata da ƴan sanda suka ambaci Sarki Sanusi II da 'Alhaji' inda ta bukaci rundunar ta nemi afuwa saboda kiransa da wannan suna da rage ma shi daraja
Buba Galadima ya ce idan wasu za su yi amfani da kotu wajen sauke mai martaba Muhammadu Sanusi II daga sarautar Kano sau 10 za su mayar da shi mulkin Kano.
Buba Galadima ya ce 'yan sanda sun gayyaci mai martaba Sanusi II ne Abuja domin a rufe shi a saka dokar ta baci a jihar a nada sabon sarki, Aminu Ado Bayero.
Duk da ba a gama shari'ar masarauta a Kano ba, Sarki Muhammadu Sanusi II, ya yi sababbin nade-nade a jihar, ciki har da ɗansa Adam Lamido Sanusi (Ashraf).
Sarkin Kano Muhammad Sanusi Ii
Samu kari