Yayin Ziyarce Ziyarce da Mai Martaba Ke Yi, Sanusi Ii Ya Ziyarci Tsohon Shugaban Kasa

Yayin Ziyarce Ziyarce da Mai Martaba Ke Yi, Sanusi Ii Ya Ziyarci Tsohon Shugaban Kasa

  • Mai Martaba Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi, ya kai ziyara ga tsohon shugaban kasa Janar Abdulsalami Abubakar a London ranar Asabar 19 ga Afrilu
  • Sun tattauna kan harkokin da suka shafi ci gaban kasa, hadin kai da ci gaba da goyon bayan tsarin mulkin dimokuradiyya a Najeriya
  • Sanusi ya nuna girmamawa ga Abdulsalami bisa rawar da ya taka wurin mika mulki da kuma kokarinsa wajen zaman lafiya a kasar nan
  • Hotunan ganawar sun karade kafafen sada zumunta, inda jama’a da dama suka yaba da wannan ganawa mai cike da mutuntaka da tarihi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Dr. Muhammad Sanusi II, ya ziyarci tsohon shugaban kasar Nigeria Janar Abulsalami Abubakar a birnin London ranar Asabar.

Ziyarar ta faru ne a ranar 19 ga Afrilu, 2025, inda suka gana domin tattaunawa kan makomar Najeriya da ci gaban kasar gaba daya.

Sanusi II ya gana da tsohon shugaban kasa
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya ziyarci tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar a London. Hoto: Sanusi II Dynasty.
Asali: Facebook

Sanusi II ya gana da Janar Abdulsalami Abubakar

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shafin Sanusi II Dynasty ya wallafa a manhajar Facebook a ranar Asabar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanusi ya nuna matukar girmamawa ga tsohon shugaban, yana yabawa da kokarinsa wajen tabbatar da zaman lafiya da mulkin dimokuradiyya a Najeriya.

Hotunan ziyarar sun bayyana a kafafen sada zumunta, inda jama’a suka nuna jin dadinsu da wannan ganawa mai cike da darasi da tarihi.

Sanusi II ya gana da tsohon shugaban kasa
Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi wata tattaunawa da tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar. Hoto: Sanusi Lamido Sanusi.
Asali: Twitter

Martanin yan Najeriya kan ziyarar Sarki Sanusi II

Masu ta'ammali da kafofin sadarwa sun yi martani kan ziyarar Sarki Sanusi II ga Janar Abdulsalami Abubakar a London.

Wasu daga cikinsu sun yi ta yi masa fatan alheri da kuma addu'o'in ci gaba da samun nasarori.

Sai dai wasu ko sun bayyana takaici da cewa basaraken ya je ne domin yin godiya saboda hana amsa gayyatarsa zuwa Abuja da yan sanda suka yi.

Russell Bobby:

"Lalle me ye tsohfaffin shugabanninmu duk ya ke yi a Landan, bayan an wawure kuma lokacin ku ya wuce."

Zeus Bilyamin El Chappo:

"Allah ya karama Sarki lafiya."

Yakubu Zakss:

"Ya je ya yi masa godiya a kan hanawa da suna yi yan sanda su bincike shi kenan."

Lawal A Sadiq:

"Ka ji manya ashe ba su ma kasar dole mu ci ubanmu."

Umar Muhammad Sanusi:

"Hmmm Abdulsalami yana hutawa a London ya gagara kawo ci gaba a Najeriya domin ya huta a nan, a karshe kuma a Najeriya za a binne shi."

Abdulrazak Kabir:

"Sarki yana bin manya don kare karagarsa."

Kungiya ta soki yan sanda kan gayyatar Sanusi II

A baya, kun ji cewa wata Kungiya ta bukaci ’yan sanda su nemi afuwa saboda cewa “Alhaji Sanusi” maimakon “Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi II”.

Mai magana da yawun kungiyar, Nura Ali ya ce hakan raini ne da cin mutunci ga matsayin Sarautar Kano da tarihinta a Arewacin Najeriya.

Kungiyar ta kuma gargadi ’yan sanda da ka da su bari siyasa ta rinjaye aikinta na kare rayuka da dukiyoyi tare da mutunta shugabannin gargajiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.