Jihar Rivers
Wasu mahara da ake zargin ƴan fashin teku ne sun farmaki jiragen ruwa guda 3, sun sace fasinjoji 13 a yankin karamar hukumar Okrika a jihar Ribas jiya Talata.
Gwamnonin PDP sun samu komawa a ƙarar da suka kalubalanci matakin Tinubu na ayyana dokar ta ɓaci a Ribas, gwamnan Delta ya janye daga ƙarara bayan =a koma APC.
Ana ta kokarin sulhu da Siminalayi Fubara, rikici ya sake kunno kai a jihar Rivers yayin da yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Gwamnn da Nyesom Wike ta rushe.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa an taso shugaban kasa, Bola Tinubu a gaba kan sanya dokar ta-ɓaci a Rivers, ana rokonsa ya dawo da Sim Fubara karshen watan Mayu.
Minista Abuja, Nyesom Wike ya zargi gwamna Siminalayi Fubara kan raina Remi Tinubu da aka yi a wajen wani taro a Rivers. Wike ya gargadi Fubara da mogoya bayansa.
Rahotanni sun ce Hukumar EFCC na binciken tsofaffin shugabannin NNPC ciki har da Mele Kyari da wasu daraktocin matatun mai bisa zargin batar da N80bn.
Fubara ya dawo daga hutun makonni biyu, bayan ya gana da Tinubu a Landan. An ce gwamnan da aka dakatar ya kuma gana da Wike, ya durkusa har gwiwa yana neman gafara.
Yayin da Remi Tinubu ke gudanar da shirin tallafawa mata, wasu sun fita daga wajen taron tallafa musu da ake yi karkashin matar shugaban kasa a Port Harcourt.
Tsohon shugaban PDP na Anambra, Cif Ndubuisi Nwobu, ya caccaki Nyesom Wike kan kasancewa a jam’iyyar APC tare da goyon bayan gwamnatin Bola Tinubu.
Jihar Rivers
Samu kari