Jam'iyyar PDP
Jigon APC, Cif Tony Okocha ya ce Nyesom Wike ya bada gudumuwa wajen nasarar Bola Ahmed Tinubu a 2023, saboda haka ya ke so jagoran PDP ya sauya-sheka zuwa APC.
Godwin Obaseki da Bukola Saraki sun halarci taron sulhun PDP. Amma ba a ga keyar Prince Uche Secondus, Nyesom Wike, Ifeanyi Ugwuannyi da Aminu Tambuwal ba.
Kungiyar majalisar jiha na APC ta bukaci Gwamna Sim Fubara da ya baiwa tsohon gwamnan Ribas Nyesom Wike yancin yanke shawara kan abun da ya shafi siyasarsa.
Wata babbar kotun tarayya mai zamanta a birnin tarayya Abuja ta mayar da tsigaggen tsohon mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Mahadi Aliyu Gusau, kan muƙaminsa.
Babban jigon jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Bode George ya yi magana kan batun komawarsa zuwa jam'iyyar APC, inda ya ce Tinubu ba makiyinsa ba ne.
Tsohon Gwamnan Benuwai ya bar hannun EFCC bayan shafe awa 10 a hannu. A cikin tsofaffin Gwamnonin da su ka sauka daga mulki, na jihar Benuwai aka fara cafkewa.
Gwamna jihar Filato, Barista Caleb Mutfwang, na jam'iyyar PDP ya amince da naɗin mutane 4 a matsayin manyan Sakatarori, mako biyu bayan korar waɗanda ya gada.
Na kusa da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bayyana cewa yawan ta'ammala da barasa shi ne ya haifarwa da Wike matsala a cikinsa.
Kotun karar zaben gwamnan jihar Osun, a ranar 19 ga watan Yuli ta yi fatali da karar da jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ta shigar kan jam'iyyar APC.
Jam'iyyar PDP
Samu kari