An Fara Maganar Shigowar Tsohon Gwamna Wike Daga PDP Zuwa Jam’iyyar APC

An Fara Maganar Shigowar Tsohon Gwamna Wike Daga PDP Zuwa Jam’iyyar APC

Cif Tony Okocha ya ce Nyesom Wike ya bada gudumuwa wajen nasarar Bola Ahmed Tinubu a 2023

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

A matsayinsa na jagoran jam’iyyar APC a Ribas, ‘dan siyasar ya ce su na yin maraba da tsohon Gwamnan

Wike ya fito ya yaki Atiku Abubakar, Okocha ya na ganin ya cancanci gwamnatin Tinubu ta tafi da shi

Rivers - Wani daga cikin jagororin jam’iyyar APC a jihar Ribas, Tony Okocha ya nuna a shirye su ke su karbi Nyesom Wike daga PDP.

Punch ta rahoto Cif Tony Okocha ya na fadawa manema labarai a garin Fatakwal cewa za su so tsohon Gwamnan Ribas ya sauya sheka.

Tsohon shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin na jihar Ribas ya yi magana ne ganin ana rade-radin cewa Nyesom Wike zai bar PDP.

Kara karanta wannan

Tsohon Minista Ya Yabi Tinubu a Kan Irin Nade-Naden Mukaman da Yake Yi a Mulki

Wike.
Wike tare da Jam’iyyar APC Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Okocha shi ne wanda ya jagoranci kungiyar BAT-Vanguard ta magoya bayan Bola Ahmed Tinubu Vanguard a Kudu maso kudancin Najeriya.

Wike ya taimaki APC a zaben 2023

‘Dan siyasar yake cewa Wike ya taka rawar gani wajen ganin Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya yi nasara a zaben bana, har ya hau kan mulki.

A cewar Okocha, akwai wasu da su ka yi watsi da Tinubu a lokacin da yake tsakiyar bukatarsa, sai yanzu su ka dawo su na ta rabar fadarsa.

“A jagorancin Bola Tinubu a reshen Ribas, mu na zaune lafiya kalau 100% da Mai girma tsohon Gwamna, Nyesom Wike a matsayin shugabanmu.
Kuturu da kudinsa, alkaki sai na kasan kwana. A lokacin da abubuwa su ka yi wahala, babu wanda zai ba mu kudin taro, sai wani ya taimaka mana.

Kara karanta wannan

“APC Ta Shirya Tarban Wike”, Majalisar Jiha Ta Magantu, Ta Fada Ma Gwamna Fubara Abun da Zai Yi

Kyau Wike ya shigo da wuri - Okocha

Ganin lokaci ya na tafiya, jaridar ta rahoto Okocha ya na cewa kyau Wike ya shigo APC tun wuri domin ya sha lagwadar gwamnati kafin ayi nisa.

Cif Okocha da mutanensa sun sallama shugaban kasa ya zabi Wike idan an tashi rabon mukamai.

Idan ana maganar ‘yan siyasar da su ka taimakawa APC a zaben shugaban kasa, jagoran jam’iyyar mai-ci ya ce babu kamar tsohon Gwamnan jihar.

Nadin Ministocin Tinubu

Za a iya samun matsala a APC tsakanin Gwamnonin Arewa da su ka bar mulki da Bola Tinubu kamar yadda rahoto ya fito a karshen makon nan.

Tsofaffin Gwamnoni sun yi bakin kokarinsu wajen ganin Jam’iyyar APC ta zarce. Amma an ji Tinubu ya fi sha’awar ya nada wadanda su ka san aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel