Atiku Abubakar Ya Yi Martani Ga Tsohon Gwamna Wike Bisa Ikirarin Cewa An Sanya Masa Guba a Sakatariyar PDP

Atiku Abubakar Ya Yi Martani Ga Tsohon Gwamna Wike Bisa Ikirarin Cewa An Sanya Masa Guba a Sakatariyar PDP

  • An bayyana tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Ezenwo Wike, a matsayin wanda yake ta'ammali da barasa fiye da ƙima
  • Phrank Shuaibu, wani hadimin Atiku Abubakar, ya yi fatali da batun sanya guba da tsohon gwamnan ya ce an taɓa yi masa
  • Ya bayyana cewa ba a sanya wa Wike guba kamar ya yi iƙirari, face kawai yawan shan barasarsa ne ya lalata masa kayan ciki

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - An gaya wa tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike cewa kayan cikinsa sun lalace ne a dalilin yawan ta'ammalin da yake yi da barasa, ba da guba guba ba kamar yadda ya yi iƙirari.

Phrank Shaibu wani hadimin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, shi ne ya yi martani ga Wike inda ya buƙace shi da bayyana ta'asar da ya tafka a lokacin zaɓen shugaban ƙasa da ya wuce.

Kara karanta wannan

"Duk Su Na Masifar Ƙaunata": Matashi Mai 'Yan Mata Biyu Ya Rasa Ta Zaba, Ya Koma Neman Taimako

Atiku ya yi martani kan batun sanya wa Wike guba
Atiku da Wike sun dade basa ga maciji Hoto: Atiku Abubakar, Nyesom Ezenwo Wike
Asali: Facebook

A cewar Sahara Reporters, ya bayyana cewa:

"Kamata ya yi gwamna Wike yana fayyace sirrikan da ya ɓoye ba wai shirya taron godiya ba. Wike bai nuna wata alamar nadama ba kan ɗumbin laifukan zaɓen da ya tafka."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Idan ba a manta ba a wajen wani taron harkokin coci a birnin Port Harcourt ranar Lahadi, 18 ga watan Yuni, Wike ya bayyana cewa kayan cikinsa irinsu ƙoda da hanta sun samu matsala a shekarar 2018 lokacin da ya yi zargin an sanya masa guba.

Wike ya bayyana cewa an sanya masa gubar ne a sakatariyar jam'iyyar PDP ta ƙasa, inda ya yi nuni da cewa kowa ma abin zargi ne.

Shaibu ya yi nuni da ta'ammali da barasa ne ya haifar da illa ga Wike

Da yake martani kan iƙirarin da Wike ya yi, Shuiabu ya bayyana cewa yawan ta'ammali da barasa da Wike yake yi ne ya yi sanadiyyar lalacewar kayan cikin nasa.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya Faɗi Babban Jigon da Alamu Suka Nuna Zai Koma APC, Ya Roƙe Shi Alfarma 1

A cewar rahoton ThisDay, ya bayyana cewa:

“Gwamna Wike ya sha nuna tsantsar ƙaunar da yake yiwa barasa. Ni ba likita bane amma abu ne wanda kowa ya sani cewa yawan shan barasa yana kawo hawan jini, ciwon zuciya, matsalar ƴan hanji da sankarar mama, baki, maƙwogoro, hanta, hanji da dubura."

Gwamna Fubara Ya Nemi Wike Alfarma

A wani labarin, gwamnan jihar Rivers Siminalayi Fubara ya miƙa ƙoƙon bararsa ga tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike, kan kada ya yi nisa da shi ko da ya sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP.

Gwamnan ya yi wannan kiran ne bayan alamu na ta ƙara nuni da cewa akwai yiwuwar Wike ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel