Tsohon Gwamnan PDP Ya Yi Maganar Farko Da Ya Shiga Hannun Hukumar EFCC

Tsohon Gwamnan PDP Ya Yi Maganar Farko Da Ya Shiga Hannun Hukumar EFCC

  • A halin yanzu Hukumar EFCC ba ta rike da Samuel Ortom wanda ake tunanin ana binciken shi
  • Bayan fiye da sa’o’i 10 ya na amsa tambayoyi domin a ji dadin bincike, ‘dan siyasar ya koma gida
  • EFCC ta yi gum har zuwa yanzu, ba za a iya cewa ga abin da ya kai Ortom hedikwatar ta ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Benue - Maganar da ake yi, Samuel Ortom yar bar hannun jami’an hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa.

Vanguard ta ce tsohon Gwamnan ya shaki iskar ‘yanci dazu ne bayan da ya dauki sama da awanni 10 a ofishin EFCC a dalilin gayyatarsa da aka yi.

Samuel Ortom ya amsa tambayoyi game da abubuwan da su ka faru a lokacin ya na Gwamna, ya yi mulki na shekaru takwas daga 2015 zuwa 2023.

Kara karanta wannan

Jigon PDP Bode George Zai Koma Wajen Tinubu a APC? Gaskiya Ta Bayyana

Bola Tinubu, Wike, Ortom
Bola Tinubu da tsohon Gwamnonin PDP 'Yan G5 Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Bayan tsawon lokaci ya na tsare a ofishin hukumar da ke Makurdi a jihar Benuwai, da kimanin karfe 7:55 aka hangi tsohon Gwamnan ya fice a mota.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A daidai lokacin da ya fito, abokan siyasa da magoya baya sun tare a wani otel su na sauraronsa. An ce 'dan siyasar ya fice ne a wata mota kirar 'SUV'

Daily Post ce Hadimin tsohon Ministan, Terver Akase ya fitar da jawabi dazu inda ya ce zargin cewa hukuma ta cafke mai gidansa ba gaskiya ba ne.

Mista Akase ya ce EFCC ta gayyaci Ortom ne, shi kuma ya amsa goron gayyatar. Shi dai tsohon Gwamnan bai fito ya yi wata magana da bakinsa ba.

"Ba a cafke Cif Ortom ko a tsare shi babban Hedikwatar EFCC da yake garin Makurdi ba.
Tsohon Gwamnan ya saba fada cewa a shirye yake da ya amsa tambayoyin masu bincike domin bai da abin da zai boye game da lokacin mulkinsa."

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar Ya Yi Martani Mai Zafi Ga Wike Bisa Ikirarin Cewa An Sanya Masa Guba a Sakatariyar PDP

- Terver Akase

Duk da ana ta bada sanarwa iri-iri a kan cafke wadanda ake zargi da laifi, zuwa yanzu babu jami’in EFCC da ya fito ya yi karin-haske a kan lamarin.

A cikin tsofaffin Gwamnonin da su ka bar ofis, na jihar Benuwai aka fara tsarewa. Babu mamaki nan gaba binciken ya shafi tsofaffin abokan aikinsa.

A hana tsofaffin Gwamoni mukamai

Labari ya zo cewa kungiyar Northern Progressives Union (NPU) ta yi kira ga Bola Ahmed Tinubu cewa ya fita daga harkartsofaffin Gwamnonin Arewa.

Shugaban NPU, Mohammed Ibrahim Kiyawa ya ce akwai tsofaffin Gwamnonin da sun ci amanar APC kuma babu abin da za su iya a kujerrar Minista.

Asali: Legit.ng

Online view pixel