Bode George Ya Yi Magana Kan Batun Komawarsa Jam'iyyar APC

Bode George Ya Yi Magana Kan Batun Komawarsa Jam'iyyar APC

  • Babban jigo a jam'iyyar PDP, Bode George, ya yi magana kan batun cewa yana shirin tsallakawa zuwa jam'iyyar APC da gwamnatin Shugaba Tinubu
  • Ɗan siyasar na jihar Legas ya ce duk da bai taɓa zama maƙiyin Tinubu ba, suna da bambance-bambancen ra'ayin siyasa sannan ba zai taɓa komawa APC ba
  • Bode ya ce dole ne a sauya fasalin Najeriya a dai na amfani da kundin tsarin mulkin da ya yi kama da na soja a mulkin dimokuraɗiyya

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Cif Bode George, ya yi tsokaci kan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu inda ya ƙara da cewa bai taɓa zama maƙiyin shugaban ƙasar ba.

Jagoran na jam'iyyar PDP ya kuma yi fatali da batun cewa akwai yiwuwar ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC) nan da wasu ƴan kwanaki duba da irin tagomashin da jam'iyyar ke samu a kwana-kwanan nan.

Kara karanta wannan

Dan Majalisar Jam'iyyar Labour Ya Ba Wa Peter Obi Shawarar Abin Da Ya Dace Ya Yi Wa Tinubu

Bode George ya yi magana kan batun komawa APC
Bode George da shugaba Tinubu Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Bode Goerge ya yi magana ne dai lokacin da bayyana a cikin shirin gidan talabijin na Channels Tv mai suna Politics Today a ranar Talata, 20 ga watan Yunin 2023.

Ya yi duba zuwa tarihi inda ya yi magana kan abinda ya faru a shekarar 1998, lokacin da Janar Abdulsalami Abubakar zai bar mulki, da kundin tsarin mulkin da aka kawo wanda ya yi kama da na sojoji saboda an shirya shi daga sama zuwa ƙasa a fannin mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kundin tsarin mulkin Najeriya ya yi kama da na mulkin soja, a cewar Bode George

Jigon na jam'iyyar PDP ya kuma yi bayanin cewa a inda ake mulkin dimokuradiyya na gaske, mulki yana farawa ne daga ƙasa zuwa sama."

George ya yi misali da yadda tsarin gwamnatin Amurka yake wanda Najeriya ta kwaikwaya, inda ya ce a ƙasar Amurka, gwamnatin jiha ita ce ta ke kula da albarkatun jiharta domin amfanar al'umma.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar Ya Yi Martani Mai Zafi Ga Wike Bisa Ikirarin Cewa An Sanya Masa Guba a Sakatariyar PDP

Shugaba Tinubu Ya Yi Wa Shettima Sabon Gata

A wani labarin shugaban ƙasa Bola Aɓmed Tinubu, ya amince da mayar da wasu manyan hukumomi guda biyu zuwa ƙarƙashin ofishin mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima.

Shugaba Tinubu ya kuma amince da yi wa ofishin na Shettima garabawul domin ƙara bunƙasa ayyukansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel