Jam'iyyar PDP
Sanata Wabara ya yi kira ga shugaba Bola Tinubu kan magance rikicin dake tsakanin Wike da Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara domin kada ya wuce gona da iri.
Duk da kokarin Bola Tinubu kan sulhunta rikicin Nyesom Wike da Siminalayi Fubara abin ya ci tura bayan sake nada sabon shugaban Majalisar jihar a yau.
Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi hukunci kan shirin da PDP ke yi na tsige shugabanta na kasa, Umar Damagun. Kotun ta haramtawa jam'iyyar daukar wannan mataki.
Jam'iyyar PDP ta magantu kan kiran da APC ta yi ga majalisar dokokin Rivers na tsige Siminalayi Fubara daga kujerar gwamnan jihar. PDP ta ce kalaman tunzurarwa ne.
Kungiyar kananan hukumomin Najeriya (ALGON) reshen jihar Rivers ta goyi bayan kiran a tsige gwamnan jihar, Siminalayi Fubara, da jam'iyyar APc ta yi.
A cikkn kwanaki kalilan da suka gaba, jam'iyyar PDP a jihar Abia ta rasamanyan kusoshi ciki har da tsohon kakakin majalisar dokokin jihar da tsofaffin mambobi.
Jam'iyyar APC reshen jihar Ribas ta umurci majalisar dokokin jihar ta fara shirin tsige Gwamna Siminalayi Fubara daga kan madafun iko ba tare da ɓata lokaci ba.
Gwamna Siminialayi Fubara na jihar Rivers ya yi barazanar wofantar da 'yan majalisar dokokin jihar yana mai cewa wanzuwar ‘yan majalisar ta ta'allaka ga amincewarsa.
Jam'iyyun PDP da APC a jihar Edo sun tafka asara na rashin 'yan takarar gwamna a jihar bayan sun yi murabus daga jam'iyyar tare da bayyana dalilansu.
Jam'iyyar PDP
Samu kari