“Ban San da Zamanku Ba”, Fubara Ya Yi Kakkausar Suka ga ’Yan Majalisar Rivers

“Ban San da Zamanku Ba”, Fubara Ya Yi Kakkausar Suka ga ’Yan Majalisar Rivers

  • Gwamnan jihar Rivers, Siminialayi Fubara ya yi kakkausar suka kan 'yan majalisar jihar yayin da sabani a tsakaninsu ke kara tsamari
  • Fubara wanda ya ce babu wasu mambobi a majalisar jihar, ya kuma ce wanzuwar ‘yan majalisar ya dogara ne ga amincewarsa
  • Gwamnan Ribas ya ce ya danne zuciyarsa kan rikicin siyasar jihar duk da karfin da yake da shi amma dayan bangaren bai yi hakan ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Siminialayi Fubara, gwamnan Rivers, ya ce wanzuwar ‘yan majalisar dokokin jihar ya ta'allaka ne ga amincewarsa ko akasin hakan.

Jaridar The Cable ta ruwaito Fubara ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin karbar bakuncin shugabannin siyasa da na gargajiya daga jihar a gidan gwamnati.

Kara karanta wannan

Majalisar dokokin Ribas ta yi wa gwamnan PDP barazana, ta amince da ƙarin kudiri 1

Fubara ya soki 'yan majalisar jihar Rivers
Gwamna Siminialayi Fubara ya yi barazanar wofantar da 'yan majalisun jihar Rivers. Hoto: @SimFubaraKSC
Asali: Twitter

Fubara yana dagawa 'yan majalisar Ribas kafa

Gwamnan Rivers ya ce babu mambobi a majalisar jihar, yana mai cewa ya yanke shawarar "daga masu kafa" saboda yarjejeniyar zaman lafiya da Shugaba Bola Tinubu ya kaddamar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fubara ya ce ya amince da yarjejeniyar zaman lafiya ne bisa fahimtar cewa akwai alaka tsakaninsa da ‘yan majalisar dokokin jihar, rahoton Channels TV.

Gwamnan Rivers ya ce ya kawar da kai a rikicin siyasar da ya dabaibaye jihar duk da karfin da yake da shi, inda ya ce dayan bangaren bai nuna hakan ba.

"Zan iya wofantar da su" - Fubara

Ya koka da cewa a kullum magoya bayansa na fuskantar barazana da kai hare-hare a jihar.

"Wadancan rukunin mutanen da ke da'awar cewa 'yan majalisarmu ne ba 'yan majalisa ba ne, a wajena ba su wanzu ba.

Kara karanta wannan

"Babu laifin Tinubu": Mataimakin kakakin majalisa ya magantu kan matsin tattali

"Ni ne nan na kyale su har suke jin kansu sun isa a kan komai, sai dai da zan ga dama yanzu, da na wofantar da su gaba daya."

- Simi Fubara

Wa ke jagorantar Najeriya a yanzu?

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito jagoran 'yan adawa a Najeriya, Atiku Abubakar ya nuna damuwa kan yadda Bola Tinubu da Kashim Shettima suka bar Najeriya lokaci daya.

Atiku ya wanda ya yi tambayar "wa ke jogarantar Najeriya a yanzu?" ya yi magana ne yayin da Shettima ya shirya zuwa Amurka alhalin Tinubu bai dawo kasar ba tun bayan zuwansa Saudiya.

Sai dai rahotanni daga baya sun bayyana ce Shettima ya fasa zuwa Amurka sakamakon matsalar jirgin sama da aka samu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel