"Ko a Jikina": Gwamna Ya Ce Ko Gezau Kan Tururuwa da Jiga jigan PDP Ke Yi Zuwa APC

"Ko a Jikina": Gwamna Ya Ce Ko Gezau Kan Tururuwa da Jiga jigan PDP Ke Yi Zuwa APC

  • Yayin jiga-jigan jam'iyyar PDP ke sauya sheka zuwa APC, gwamnan Abia, Alex Otti ya yi martani kan lamarin
  • Gwamnan ya ce ko kadan hakan bai shafe shi ba tun da jam'iyyar PDP ce ke rasa jiga-jiganta zuwa APC mai mulki
  • Otti ya ce bai kamata tun yanzu a fara maganar zabe ba saboda da sauran lokaci domin tabbatar da inganta rayuwar 'yan jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Abia - Gwamnan jihar Abia, Alex Otti ya magantu kan sauya sheka da 'yan jami'iyyar PDP ke yi zuwa APC.

Gwamnan ya ce wannan abin da ke faruwa na sauye-sauyen sheka ko a jikinsa saboda ba shi ta shafa ba.

Kara karanta wannan

Katsina: Manyan dalilai 3 da suka tilastawa Shema watsar da PDP zuwa APC

Gwamna ya ce bai damu da sauya sheka da jiga-jigan PDP ke yi zuwa APC ba
Gwamna Alex Otti ya nuna rashin damuwa kan yadda 'yan PDP ke tserewa zuwa APC a jihar. Hoto: Alex Otti.
Asali: Facebook

Gwamnan Abia ya magantu kan watsewar 'yan PDP

Otti ya ce jam'iyyar PDP ce ya kamata ta shiga mummunan yanayi tun da ita ke rasa mambobinta, cewar rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce jam'iyyun siyasa kamar coci suke kowa yana da ra'ayin shiga a duk lokacin da ya ga dama ba tare da matsala ba, Pulse ta tattaro labarin.

Gwamnan ya bayyana haka ne a jiya Alhamis 9 ga watan Mayu yayin ganawa da manema labarai da ya ke yi duk wata.

"Ban ga abin damuwa ba kan haka, saboda jam'iyyun siyasa kamar coci suke duk inda kaga dama zaka shiga ba mai hana ka."
"Ban damu ba ko kadan saboda ba jam'iyya ta suke bari ba, nima akwai wadanda ke shigowa jam'iyya ta kuma wasu da yawa suna zuwa a gaba."
"Zaka iya shiga jam'iyya ko ka fita a duk lokacin da kaga dama, babu tunanin zaben tun yanzu saboda ya yi wuri a fara wannan magana."

Kara karanta wannan

Harajin CBN: Na hannun daman Tinubu ya fadi abin da 'yan Najeriya ya kamata su yi

- Alex Otti

Gwamna Otti da tabbacin raya al'umma

Otti ya ce baban abu mafi muhimmanci a yanzu shi ne samarwa 'yan jihar shugabanci nagari kamar yadda aka musu alkawari.

Wanann na zuwa ne bayan jiga-jigan jam'iyya PDP sai watsewa suke yi zuwa APC duk da kasancewar gwamnan ɗan jam'iyyar LP.

Tsohon gwamnan Imo ya bar PDP

A wani labarin, an j tsohon gwamnan jihar Imo, Emeka Ihedioha ya yi murabus daga jam'iyyar PDP saboda rashin tsari a tafiyar da ake aiki.

Ihedioha ya ce kwata-kwata jam'iyyar ba ta shirya yin adawa mai karfi ba ga jam'iyyar APC mai mulki ganin yadda kamun ludayinta ya ke.

Asali: Legit.ng

Online view pixel