Zaben 2027: "'Yan Adawa na Gagarumin Shirin Kifar da Gwamnatin APC", Utomi

Zaben 2027: "'Yan Adawa na Gagarumin Shirin Kifar da Gwamnatin APC", Utomi

  • Masanin tattalin arzikin siyasa a Najeriya, Pat Utomi ya ce ana gagarumin shirin hadakar jam’iyyu domin samar da adawa mai karfi a zaben 2027
  • Ya fadi haka ne jim kadan bayan dawowa Najeriya daga kasar Amurka inda ya shafe tsawon lokaci ba a ji duriyarsa a fagen siyasa ba
  • Farfesa Pat Utomi ya ce ‘yan siyasar kasar nan sun gaza kuma ba su da akidar ceto Najeriya daga mawuyacin halin da take ciki a yau

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja-Shahararren masanin tattalin arzikin siyasa a Najeriya, Farfesa Pat Utomi ya ce ana gagarumin shirin hadakar adawa mai karfi tunkarar zaben 2027.

Kara karanta wannan

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na shirin kafa jam'iyya domin lallasa Tinubu a 2027

Farfesa Pat Utomi ya bayyana haka ne jim kadan bayan dawowarsa Najeriya daga kasar Amurka da ya shafe tsawon lokaci a can.

Farfesa Pat Utomi
Ana shirin samar da adawa mai karfi ga APC a zaben 2027 Hoto: @UtomiPat
Asali: Twitter

Akwai maganar gangami a 2027 har yau?

A rahoton da Daily Trust ta wallafa, Farfesa Pat Utomi ya bayyana cewa Najeriya ba za ta samu ci gaban da take bukata a karkashin mulkin APC ko wani jam’iyyar adawa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masanin na ganin wannan na daga dalilan da wasu masu ra’ayin ci gaba za su hade wuri guda kafin zaben 2027.

“Za a ceto Najeriya a 2027,” Pat Utomi

Masanin tattalin arzikin siyasar Najeriya, Pat Utomi ya bayyana cewa tsarin siyasar Najeriya bai dace da talakawan kasar ba.

Farfesan ya bayyana cewa akwai ana shirye-shiryen samar da babbar jam’iyyar adawa gabanin zaben 2027 domin ceto Najeriya .

Kara karanta wannan

"Yana da kyau amma...": Dattawan Arewa sun bayyana matsayarsu kan harajin CBN

Ya bayyana cewa ya dawo kasar nan ne domin a karafafa shirin samar da hadakar masu ra'ayin ci gaba domin jam’iyyun siyasar Najeriya sun kasa tabuka komai, kamar Punch News ta wallafa.

“Ina da yakinin tsarin siyasar jam’iyyun Najeriya sun gaza. Babu batun dimukuradiyya a jam’iyyun siyasa, kuma basa aikinsu na hidimtawa al’umma,” inji Farfesa Utomi.

2027: Akwai yiwuwar hadaka a zaben gaba

Mun ruwaito muku cewa tsohon mai neman kujerar gwamna a jam’iyyar PDP a jihar Ogun, Dr Segun Showunmi, ya ce akwai yiwuwar jam’iyyarsa ta yi irin dabarar da APC ta yi wajen karbe ikon mulkin kasar nan daga PDP.

Dr Segun Showunmi, ya ce akwai yiwuwar jam’iyyarsa ta hade da wasu jam’iyyu domin samun karfin ikon tunbuke APC daga mulkin kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel