Fubara vs Wike: An Yi Kira Ga Bola Tinubu Ya Tsoma Baki Kan Rikicin Siyasar Jihar Rivers

Fubara vs Wike: An Yi Kira Ga Bola Tinubu Ya Tsoma Baki Kan Rikicin Siyasar Jihar Rivers

  • Rikici siyasa ya kara ƙamari a jihar Rivers yayin da yan majlisa ke kokarin tsige gwamnan jihar, Siminalayi Fubara
  • Babban jigo a jam'iyyar PDP, Sanata Adolphus Wabara ya yi kira na musamman ga shugaba Bola Tinubu kan shiga lamarin
  • Sanata Adolphus Wabara ya bayyana irin hatsarin da rikicin zai haifar da kuma yadda zai shafi Najeriya baki daya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Tsohon shugaban majalisar dattawa kuma shugaban majalisar amintattu na jam'iyyar PDP, Sanata Adolphus Wabara ya yi kira ga shugaba Bola Tinubu kan rikicin siyasar jihar Rivers.

Fubara da wike
Sanata Wabara ya nemi Bola Tinubu ya magance rikicin Rivers. Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS, Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Sanata Wabara ya yi kiran ne yayin da rikici ya yi ƙamari tsakanin ministan Abuja, Nyesom Wike da Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara.

Kara karanta wannan

Majalisar wakilai ta ki daukar matsaya kan harajin tsaron yanar gizo, 'dan majalisa ya koka

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Adolphus Wubara ya yi kiran ne a dalilin sabon rikicin da ya barke a majalisar dokoin jihar kwanan nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rikici a majalisar dokokin jihar Rivers

Rikicin ya kai ga raba kan majalisar gida biyu, bangaren gwamnan Fubara da bangaren minista Wike wanda hakan ya kai ga kira kan tsige gwamnan.

A satin da ya wuce ne dai har yanzu shugaban APC na jihar, Tony Okocha, ya yi kira ga 'yan majlisar da su gaggauta tsige gwamnan.

Rivers: Kiran sanata Wabara ga Bola Tinubu

A cikin sakon da ya aikawa shugaba Bola Tinubu, Sanata Wabara yace idan rikici ya barke a jihar Rivers zai shafi Najeriya baki daya.

Saboda haka ne ya yi kira ga Bola Tinubu kan jan hankalin ministan domin ya kyale gwamnan jihar ya yi ayyukan da ke gabansa.

Kara karanta wannan

Duk da kokarin Tinubu, Rikicin Wike da Fubara ya sake munana bayan matakin Majalisa

Kiran sanata Wabara ga yan majalisan Rivers

Har ila yau ya yi kira ga 'yan majalisar jihar kan su kaucewa tada fitina wajen yunkurin tsige gwamnan.

A cewarsa akwai hatsari mai girma da barazana ga demokradiyya wajen tsige zaɓaɓɓen gwamnan jiha.

Ya kuma tabbatar da cewa jam'iyyar PDP ba za ta zuba idon wajen ganin ana ƙoƙarin kunna rikicin siyasa a jihar Rivers ba.

Saboda haka yayi kira ga mambobin jam'iyyar wajen jajircewa domin tabbatar da sun cigaba da samun goyon baya a jihar.

Fubara vs Wike: Me ya jawo rikicinsu?

A wani rahoton, kun ji cewa Dele Momodu, jigo a babbar jam'iyyar adawa ta PDP ya bayyana dalilan barakar da aka samu tsakanin tsohon gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike da Siminalayi Fubara.

Momodu ya bayyana cewa rigimar ta kunno kai ne kan wanda zai yi iko da baitul malin jihar wacce ya yi zargin shugaba Bola Tinubu na son ya yi iko da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel