Yan wasan Kannywood
Kannywood ta yi rashin jarumi Baba Ahmadu (Hedimasta) na shirin Dadin Kowa. 'Yan Kannywood sun fito sun yi ta’aziyya, suna fatan Aljanna ce makomarsa.
Sani Danja ya samu mukamin mai ba gwamna shawara kan matasa da wasanni a Kano. 'Yan Kannywood sun taya jarumin murna tare da addu'ar Allah ya taya riko.
Jarumai mata da maza sun cika wajen bikin diyar Asma'u Sani, suna wasa, dariya, da daukar hotuna a ranar daura aure, wanda ya kayatar kwarai da gaske.
Za a dawo haska shirin Gidan Badamasi zango na shida daga ranar 19 Disambar 2024, da misalin 6:00 na yamma, tare da barkwanci da salo mai ban sha'awa.
Hadiza Gabon ta tuna marigayi El-Muaz, wanda ya rasu a bikin mawaki Auta Waziri, tana cewa radadin rashin mutanen kirki baya gushewa daga zuciya.
Mutuwar El-Mu'az Birniwa ta haddasa ce-ce-ku-ce yayin da mawakan Kannywood suka shirya casu kwanaki biyar kacal bayan rasuwarsa, abin da ya fusata Nasiru Ali Koki.
Mansura Isah ta shiga tsananin damuwa bayan 'yan damfara sun sace gaba daya kudin da ta mallaka a asusun bankunanta biyu. Tsohuwar jarumar ta ce yanzu ta talauce.
Mawaki kuma jarumi Adam A Zango ya shirya babban casu. A wani bidiyo da ya wallafa a intanet, an ga daruruwan masoya suna nishadantuwa da wakokin Zango.
Fitaccen jarumar Kannywood, Teema Yola ta wallafa bidiyon da ake kyautata zaton shi ne na karshe na mawaki El-Muaz Birniwa kafin rasuwarsa a daren ranar Alhamis.
Yan wasan Kannywood
Samu kari