Yan wasan Kannywood
Fitacciyar jarumar Kannywood, Hadiza Gabon ta daura damar yin karar wani gidan talabijin da ta ce ya sace bidiyonta tare da watsawa a tasharsa ba tare da izini ba.
Legit Hausa ta tattaro yawan mabiyan da wasu fitattun jaruman Kannywood ke da su a shafukan sada zumunta. Ali Nuhu ne mafi yawan mabiya da mutane miliyan 8.5.
Fitaccen mawakin Arewa, Naziru sarkin waka ya saki bdiiyon sabon askin kwal kwabo da ya yi. Naziru ya roki masu bibiyarsa da su kalli bidiyon amma ban da dariya.
Fitaccen mawakin siyasa, Shalelen Mawaka ya samu kyautar sabuwar moa kirar Peugeot 406 daga gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf. Mutane sun yi martani.
Mawakin APC, Dauda Kahutu Rarara ya yi wakar martani bayan goge shafinsa na Facebook da talakawa suka nema a yi a kan wakar Bola Tinubu cikin sabuwar waka.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu matasan karamar hukumar Nasarawa ta jihar Kano sun yi kira ga Sani Danja da ya fito takarar ciyaman din karamar hukumar.
Wasu daga cikin jaruman Kannywood sun fice daga NNPP zuwa APC a jihar Kano. Rabi'u Daushe, Hauwa Waraka, Alhaji Habu Tabule na cikin wadanda Barau Jibrin ya karba.
Yanzu muke samun labarin rasuwar fitaccen jarumi a masana'antar shirya fina-finan Hausa, Suleiman Alaƙa. An ce jarumi Suleiman ya rasu ne a yau Litinin, 22 ga Yuli.
Bayan bikin cika shekaru 10 da kafuwa, tashar Arewa 24 ta kawo sababbin zafafan shirye shirye guda uku da suka hada da Arewa Gen Z, Jaru Road, Climate Change Africa.
Yan wasan Kannywood
Samu kari