Majalisar dattawan Najeriya
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, yana neman mafita, zai tattauna da hukumomin kamfanin Shoprite don hana su barin jihar Kano.
Kamar yadda ya fada a dandalin Twitter, Hon. Abdulmumin Jibrin (NNPP) ya sake yin rabon tsabar kudi ga al’ummar da yake wakilta a majalisar tarayya daga Kano.
Simon Lalong ya bar majalisar ministocin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a hukumance domin ya karbi kujerar sa ta majalisar dattawa. Tinubu ya amince da murabus din.
Wasu 'yan majalisar tarayya sun dauki bangare dabam a rigimar PDP a Ribas. Boma Goodhea da Awaji-Inombek Abiante su na goyon bayan Simi Fubara a kan Nyesom Wike
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya ce likitocinsa sun tabbatar da cewar yana dauke da zazzabin cizon sauro bayan bikin cikarsa shekaru 61.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya fadi bayan kammala bikin ranar haihuwarsa a otal din Transcorp Hilton da ke Abuja a jiya Alhamis.
Rabiu Musa Kwankwaso ya yi zama da ‘Yan majalisa domin a karfafa NNPP. Kwankwaso ya tattauna da Ali Sani Madaki, Abdulmumin Jibrin da Abdulkadir Tijjani Jobe.
Bola Tinubu ya jinjinawa Godswill Akpabio da Rt. Hon. Tajudeen Abbas. Shugaban kasar ya ce samun Akpabio da Abbas a Majalisar Tarayya ne zai zama silar nasara.
Ministoci sun roki Majalisa ta kara masu kudin da za su kashe a 2024. Akalla Ministoci 3 su ka nuna kasafin kudin shekarar 2024 da aka yi ba zai je ki ina ba.
Majalisar dattawan Najeriya
Samu kari