Zaben Gwamnan Kogi Na 2023: Dino Melaye Ya Nemi a Soke Zabe a Kananan Hukumomi 5

Zaben Gwamnan Kogi Na 2023: Dino Melaye Ya Nemi a Soke Zabe a Kananan Hukumomi 5

  • Sanata Dino Melaye, dan takarar gwamnan PDP a zaben jihar Kogi ya koka kan yadda aka gudanar da zabe a yankin Kogi ta tsakiya
  • Dino ya bukaci hukumar zabe da ta soke zabe a kananan hukumomi biyar na yankin
  • A cewar tsohon dan majalisar, an tafka magudi a kananan hukumomin Okene, Okehi, Ajaoukuta, Adavi, da Ogori/Mangogo

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kogi - Dan takarar gwamnan jam'iyyar PDP a jihar Kogi, Sanata Dino Melaye, ya yi kira ga hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) da ta soke zabe a kananan hukumomi biyar na jihar.

Melaye ya ce zaben da aka gudanar a wadannan yankuna na cike da magudi na fitar hankali.

Kara karanta wannan

Labari Da Dumi: Hukumar INEC ta sanar da duka wuraren da aka soke zabe a Kogi

Dino Melaye ya nemi a soke zabe a kananan hukumomi biyar
Zaben Gwamnan Kogi Na 2023: Dino Melaye Ya Nemi a Soke Zabe a Kananan Hukumomi 5 Hoto: @_dinomelaye
Asali: Twitter

Tsohon dan majalisar tarayyar ya lissafa kananan hukumomin da yake son a soke zabe a matsayin Okene, Okehi, Ajaoukuta, Adavi, da Ogori/Mangogo – gaba dayansu a yankin Kogi ta tsakiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi kiran ne a shafinsa na dandalin X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) @_dinomelaye

"Ya zama dole INEC ta soke zabe a kananan hukumomi 5 na Kogi ta tsakiya. Zaben da aka yi a Okene, Okehi, Ajaoukuta, Adavi, da Ogori/Mangogo duk suna cike da zamba na fitar hankali."

Dino Melaye ya lashe rumfarsa

A wani labarin, mun ji cewa Sanata Dino Melaye, ɗan takarar gwamnan jihar Kogi a inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya samu nasarar lashe rumfar zaɓen da yake kaɗa kuri'a.

Tsohon mamban majalisar dattawan ya lallasa jam'iyyar APC da gagarumin rinjaye a rumfar zaɓensa da ke Iluafon quarters, RA: Aiyetoro 1, ƙaramar hukumar Ijumu a jihar Kogi.

Sanata Melaye ya samu ƙuri'u 210 a zaben da aka kaɗa yau Asabar a rumfar zaɓen inda ya lalllasa babban abokin adawarsa na jam'iyyar APC, Usman Ododo, wanda ya samu kuri'u 22.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel