"Gagarumin Magudi a Dukkan Rumfunan Zaben Kogi" Dino Melaye Ya Zargi APC Da Magudin Zabe

"Gagarumin Magudi a Dukkan Rumfunan Zaben Kogi" Dino Melaye Ya Zargi APC Da Magudin Zabe

  • Dino Melaye, ya umurci jami'an jam'iyyarsu da su nuna turjiya idan INEC ta ki nuna masu tsaftatacciyar takardar rubuta sakamakon zabe
  • Melaye, dan takarar gwamnan jihar Imo, ya yi zargin cewa jami'an hukumar zaben sun ki nuna wa jami'ansu takaradar rubuta sakamakon zaben don tantance wa
  • Ya ce an dakatar da kada kuri'a a Ogori Mangogo, inda lamarin ya faru, har sai jami'an hukumar sun nuna wa jami'ansu takarar, ko su tayar da zanga-zanga

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Lokoja, jihar Kogi – Dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Kogi, Sanata Dino Melaye, ya shaida wa wakilan jam’iyyarsa da su yi turjiya tare da yin zanga-zanga matukar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ki nuna masu tsaftatacciyar takardar rubuta sakamakon zabe.

Kara karanta wannan

Dakarun soji sun damke wasu motoci 3 da ake zargi a zaben jihar Kogi

Melaye, ya ce ba a fara kada kuri’a a Ogori Mangogo ba, saboda ma’aikatan INEC sun ki nuna takardar rubuta sakamakon zabe ga wakilan PDP.

Dino Melaye
Melaye ya ba da umurni ga wakilan jam'iyyarsu, da su yi zanga-zanga idan hukumar zabe ta ki nuna takardar sakamakon zabe Hoto: Dino Melaye
Asali: Twitter

Tsohon dan majalisar, ya bayyana hakan a shafin na X (wanda aka fi sani da Twitter) @_dinomelaye, a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“An dakatar da kada kuri’a a mazabar ogori mangogo, saboda jami'an INEC sun ki nuna wa wakilanmu tsaftatattun takardun rubuta sakamakon zabe. Idan sun ki nuna muku sahihan takardun sakamakon zaben, ku yi turjiya da zanga-zanga."

Wanda zai lashe zaben Kogi - Hasashen 'yan Najeriya

Gabanin zaben jihar Kogi, yan Najeriya a shafukan sada zumunta sun yi hasashen wanda zai yi nasara a zaɓen jin ra'ayi da Legit.ng ta gudanar a shafin Twitter.

Bayanai na INEC sun nuna cewa jam’iyyun siyasa da yan takara 18 ne ke fafatawa a zazen, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

A zaben jin ra'ayin da Legit.ng ta gudanar a shafin Twitter, 54.4% na wadanda suka yi zaben sun ce Dino Melaye, dan takarar jam'iyyar PDP ne zai lashe zaben, yayin da 26% suka zabi Usman Ahmed Ododo na jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Asali: Legit.ng

Online view pixel