Zaben Kogi: Abu Ya Fara Tsami, Dino Melaye Ya Kauracewa Zaben, Ya Fadi Dalilai Masu Rikitarwa

Zaben Kogi: Abu Ya Fara Tsami, Dino Melaye Ya Kauracewa Zaben, Ya Fadi Dalilai Masu Rikitarwa

  • Dino Melaye, dan takarar jam’iyyar PDP a zaben jihar Kogi ya kauracewa zaben da ake gudanarwa a jihar Kogi
  • Melaye na zargin an shirya magudi a zaben inda ya ce an gama komai tun kafin a fara kada kuri’u a zaben
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da kada kuri’u a zaben jihohin Bayelsa da Kogi da kuma jihar Imo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kogi - Dan takarar jam’iyyar PDP, Dino Melaye ya kauracewa zaben da ake gudanarwa a jihar Kogi.

Melaye na zargin an riga an kamala zaben tun kafin a fara kada kuri’u shi yasa ya kauracewa zaben.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an nemi Melaya an rasa a mazabarshi a rumfar 004 da ke ‘Ward’ 002 a karamar hukumar Ijumu.

The Nation ta tabbatar cewa Dino ya na gida tare da wasu daga cikin magoya bayansa inda su ka kauracewa zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel