Zaben Gwamnoni: Ana Bugawa da SDP da APC a Kogi, PDP Tayi Gaba a Bayelsa, APC a Imo

Zaben Gwamnoni: Ana Bugawa da SDP da APC a Kogi, PDP Tayi Gaba a Bayelsa, APC a Imo

  • Sakamakon zaben Gwamnonin jihohin Imo, Kogi da Bayelsa ya fara fitowa bayan mutane sun kada kuri’a a ranar Asabar
  • Babu mamaki a jihar Bayelsa, Gwamna Douye Diri ya zarce, haka kuma a Imo, Hope Uzodimma zai iya lashe zaben tazarcensa
  • Zuwa yanzu a jihar Imoana gwabzawa ne tsakanin ‘dan takaran jam’iyyar SDP da na APC, sai Dino Melaye na PDP yana na uku

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Nigeria - A zaben Gwamnonin jihohi na 11 ga Nuwamba a Imo, Kogi da Bayelsa, alamu sun nuna yadda ake gwabzawa da manyan jam’iyyu.

Punch ta ce Gwamna Douye Diri shi ne kan gaba a jihar Bayelsa yayin da takwaransa na Imo, Hope Uzodimma ya shiga gaba a zaben Gwamna.

Kara karanta wannan

Yadda Aka Shakawa Masu Zabe N40, 000 Domin a Saye Kuri’unsu a Zaben Gwamnoni

Zaben Kogi
Dino Melaye wajen shirin zaben Kogi Hoto: @_dinomelaye
Asali: Twitter

Zaben Kogi ya dauki zafi

Amma a jihar Kogi zuwa yanzu ba za a iya cewa ga wanda yake kan nasara tsakanin Ahmed Usman Ododo da kuma Murtala Yakubu Ajaka ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dino Melaye wanda yake rike da tutan jam’iyyar PDP ya na cikin manyan ‘yan takara.

PDP v APC a zaben Imo da Bayelsa

A kuri’un da aka tattara daga wasu rumfunanan zabe 130 a jihar Bayelsa, an gano Diri ya na da kuri’u 13, 396, sai Timipre Sylva ya na da 4,802.

Sakamakon da aka samu daga rumfuna 90 na Imo ya nuna Gwamna Hope Uzodinma ya na da 22, 113 sai Samuel Anyanwu na PDP mai 1452.

‘Dan takaran LP a zaben Gwamnan, Sanata Athan Achonu ya na gaban PDP da 1,658.

Zaben Kogi: SDP, PDP na bin APC

Kara karanta wannan

Labari Mai Zafi: DSS da EFCC Sun Dura Rumfar da Dino Melaye Zai Dangwala Kuri’a

Daga rumfunan da aka fara samun fitowar sakamako, Adodo ya samu kuri’u 21,047, sai Ajaka ya na da 7, 324, sai Dino da PDP mai kuri’u 2,529.

Muri Ajaka ne ya ke yin galaba a rumfunan zaben Kogi ta gabas, hakan ya tabbata da hasashenmu na cewa kabilanci zai yi tasiri a takarar bana.

An tsaida zaben Gwamna a Kogi

Ana da labari sanarwa ya fitoinda aka ji INEC ta ce ba za ta yarda da yadda sakamako ya fito tun kafin a fara dangwala kuri’u a zaben jihar Kogi ba.

Yunkurin magudin ya auku a kananan hukumomin Adavi, Ajaokuta, Ogori/Magongo, Okehi da Okene, saboda haka aka tsaida yin zabe a wuraren.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng