Dino Melaye Ya Kauracewa Zaben Gwamnan Kogi? Gaskiya Ta Bayyana

Dino Melaye Ya Kauracewa Zaben Gwamnan Kogi? Gaskiya Ta Bayyana

  • Dan takarar jam'iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Kogi, Sanata Dino Melaye, ya yi watsi da rade-radin cewa shi da magoya bayansa sun kauracewa zaben da ake gudanarwa
  • Melaye ya dage cewa shi ya kada kuri'arsa amma dai ya ki fadin mazabar da ya kada kuri'ar tasa
  • Tun farko dai tsohon sanatan ya yi zargin cewa an tafka magudi a zaben inda ya ce an samu bullar sakamakon zabe a wasu wuraren tun kan a gama kada kuri'a

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Lokoja, Jihar Kogi - Sanata Dino Melaye, dan takarar jam'iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Kogi da ke gudana, ya karyata rahotannin cewa ya kauracewa zaben gwamna da ke gudana a jihar.

Kara karanta wannan

Labari Da Dumi: Hukumar INEC ta sanar da duka wuraren da aka soke zabe a Kogi

A wata wallafa da jaridar TheCable ta yi a dandalin X, dan takarar na PDP ya karyata ikirarin amma ya ki bayyana a inda ya kada kuri'arsa a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba.

Sanata Dino Melaye ya karyata rade-radin cewa bai kada kuri'u ba
Dino Melaye Ya Kauracewa Zaben Gwamnan Kogi? Gaskiya Ta Bayyana Hoto: Dino Melaye
Asali: Twitter

Da farko an rahoto cewa Melaye ya kauracewa zaben da aka yi a fadin kananan hukumomi 21 na jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, ba a ga tsohon sanatan ba a rumfar zabensa mai lamba 004, gudunma ta 002 a kwatas din Iluafon, Aiyetoro Gbede, karamar hukumar Ijumu don kada kuri'arsa.

An rahoto cewa dan takarar na PDP ya kasance a mahaifarsa tare da wasu mutane amma aka ce sun kauracewa tsarin.

INEC ta magantu kan bullar sakamako

A wani labarin, mun ji cewa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ce tana sane da gano bullar takardun sakamakon zabe da aka cika a wasu rumfunan zabe a zaben gwamna da ke gudana a jihar Kogi.

Kara karanta wannan

Zaben Imo: Ina da kwarin gwiwar cewa zan yi nasara, dan takarar PDP, Anyanwu

A cikin wata sanarwa da hukumar zaben ta fitar a dandalinta na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya, ta ce an ja hankalinta zuwa ga wani rahoto da ke nuna an samu bullar sakamakon zaben.

Sai dai kuma, hukumar INEC ta tabbatar da cewar ta dauki lamarin da muhimmanci kuma za ta dauki mataki a kai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel