Hukumar yan sandan NAjeriya
Rundunar yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da dakile wani yunkurin yin garkuwa da mutane da yan bindiga suka yi tare da halaka mutum uku daga cikinsu.
Sakamakon hare-haren 'yan bindiga, mutanen kauyen Yewuti da ke babban birnin tarayya Abuja sun yi hijira zuwa makwaftan garuruwa. Yan bindiga sun kashe mutum daya.
Mr. Samuel Soyemi ne ya ba da labarin yadda wasu jami'an 'yan sanda suka sace shi da iyalinsa tare da karbar Naira miliyan daya da kwashe wasu kayayyaki.
Yan sanda sun kama Somadina Orji mai shekaru 25 kan zargin kashe mahaifiyarsa, Misis Charity, da kanwarsa Miss Ukamaka, sannan ya binne su a karamin rami a gidansu.
Wani magidanci ya shiga hannun jami'an tsaro bayan ya yi yunkurin halaka matarsa har lahira. Jami'an yan sanda sun tabbatar da cafke shi a jihar Bauchi.
Iyalan dalibin jami'ar jihar Ebonyi da ayarin motocin gwamnan jihar Ebonyi suka halaka na neman ayi musu adalci yayin da yan sanda ke yin rufa-rufa.
Jami’an yan sanda sun kama wani matashi dan shekaru 17 Lawali Mori kan zargin lalata da zakata a kauyen Viniklang, karamar hukumar Girei ta jihar Adamawa.
Kotun yanki a Jos da ke jihar Plateau ta daure matashi mai suna Jemilu Bala watanni shida a gidan gyaran hali kan zargin satar Maggi da kuma sabulu.
Gwamnatin jihar Ogun ta sanar da sanya ladan N50m ga duk mutumin da ya taimaka bayanan sirri har aka kama yan bindigan da suka kashe daraktan kuɗi.
Hukumar yan sandan NAjeriya
Samu kari