Nasara Daga Allah: Yan Sandan Sun Dakile Harin Yan Bindiga, Sun Kashe Mutum 3

Nasara Daga Allah: Yan Sandan Sun Dakile Harin Yan Bindiga, Sun Kashe Mutum 3

  • Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta samu nasarar daƙile wani harin ƴan bindiga a kan hanyar Dutsinma zuwa Kankara
  • Jami'an ƴan sandan tare da haɗin gwiwar ƴan banga sun kuma yi nasarar halaka ƴan bindiga uku a yayin artabun
  • Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Katsina shi ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta ce ta dakile wani yunƙurin yin garkuwa da mutane a kan hanyar Dutsinma zuwa Kankara, tare da kashe mutum uku da ake zargi.

Jaridar Premium Times ta ce kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Abubakar Sadiq-Aliyu, shi ne ya tabbatar da hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Katsina ranar Lahadi, 10 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

Jami'an DSS sun kai samame fadar babban sarki, sun kwato makamai

Yan sanda sun halaka yan bindiga a Katsina
Yan sanda sun halaka yan bindiga uku a Katsina Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

Ya bayyana cewa an samu nasarar daƙile yunƙurin yin garkuwa da mutanen da ƴan bindigan suka yi ne, a ranar Lahadi 10 ga watan Disamba, rahoton Leadership ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka fatattaki ƴan bindigan

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

“A ranar 10 ga watan Disamba, 2023, da misalin ƙarfe 4:30 na yamma, bisa samun sahihan bayanai na cewa wasu da ake zargin ƴan bindiga ne da masu garkuwa da mutane, ɗauke da muggan makamai irin su AK-47, sun tare babbar hanyar Dutsinma zuwa Kankara a kokarinsu na sace mutane."
"Bayan samun rahoton kwamandan yankin Dutsinma, nan take ya haɗa tawagar haɗin gwiwa na jami’an ƴan sanda da ƴan banga suka kai ɗauki."
"Da isar su wurin, waɗanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka bude wa jami’an wuta, inda jami’an suka yi ta maza suka mayar da wuta tare da yin nasarar kashe wasu ƴan bindiga guda uku."

Kara karanta wannan

Dakarun sojojin sama sun sheke kasurgumin dan ta'addan da ake nema ruwa a jallo

"Wani ɗan banga mai suna Masa’udu Sani, ya samu rauni a hannun damansa."

ASP Sadiq-Aliyu ya ƙara da cewa a halin yanzu Sani yana karɓar magani yayin da ake kokarin cafke sauran ƴan bindigan da suka tsere tare da cigaba da gudanar da bincike.

An Fatattaki Yan Bindiga Tare da Gwamna Radda

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ya bi sahun jami'an tsaro domin fatattakar ƴan bindiga.

Gwamnan ya bi jami'an tsaron a ƙauyen Zakka na ƙaramar hukumar Safana inda suka fatattaki ƴan bindigan tare da ceto wani mutum ɗaya da suka sace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel