Allah Sarki: Mahara Sun Sace Babban Sarki Bayan Hallaka Hadiminsa da Ya Yi Kokarin Hana Garkuwar

Allah Sarki: Mahara Sun Sace Babban Sarki Bayan Hallaka Hadiminsa da Ya Yi Kokarin Hana Garkuwar

  • Mahara sun sace babban Basarake a jihar Cross River bayan hallaka hadiminsa da ya yi kokarin kare shi
  • Maharan su kai harin ne a ranar Lahadi 10 ga watan Disamba da dare a karamar hukumar Akpabuyo da ke jihar
  • Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Irene Ugbo ya tabbatar da faruwar lamarin sai dai bai ba da cikakken bayani ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Cross River - Wasu 'yan bindiga sun kai farmaki jihar Cross River inda su ka sace mai sarautar gargajiya yayin harin.

Maharan sun yi garkuwa da Etiyin Maurice Edet a daren ranar Lahadi 10 ga watan Disamba a karamar hukumar Akpabuyo da ke jihar, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

Sojin sama sun yi ajalin kasurgumin dan ta'adda, Kachalla, sun hallaka kwamandojin Dogo Gide 3

Mahara sun sace babban Basarake da kuma hallaka hadiminsa
'Yan bindiga sun yi garkuwa da babban Basarake a jihar Cross River. Hoto: NPF.
Asali: Twitter

Wane martanin rundunar 'yan sanda ta yi kan harin?

Punch ta tattaro cewa maharan sun kuma hallaka hadimin Sarkin a kokarin kare mai gidansa yayin harin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Irene Ugbo ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce har yanzu babu cikakken bayani.

Vanguard ta tattaro cewa Ugbo bai ba da bayanin ko maharan sun bukaci kudin fansa ba ko kuma sun tuntubar iyalansa kan wannan lamari.

Farfesa ya kubuta daga hannun 'yan bindiga

Har ila yau, 'yan bindiga sun sako Farfesa Patrick Egaga da su ka yi garkuwa da shi kwanaki 24 da su ka wuce.

Egaga wanda darakta ne a Jami'ar Calabar an sace shi ne a watan da ta gabata inda maharan su ka bukaci naira miliyan 50 kudin fansa.

Birnin Calabar a cikin watanni biyu da su ka wuce na shan fama da hare-haren 'yan bindiga da su ke yin garkuwa da mutane ba kakkautawa inda su ke sace manyan mutane a birnin.

Kara karanta wannan

Tinubu ya gargadi sojojin Najeriya: "Kar ku kuskura ku kara jefa bam kan fararen hula"

Sojin sama sun sheke Kachalla da yaran Dogo Gide

A wani labarin, rundunar sojin sama ta yi ajalin wani kasurgumin dan ta'adda, Ali Alhaji Alheri yayin wani mummunan hari a jihar Niger.

Marigayin wanda aka fi sani da 'Kachalla Ali Kawaje' ya rasa ransa ne a jiya Litinin tare da wasu manyan yaran Dogo Gide.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel