Jihar Niger
An kuma asarar rayuka bayan wani hatsarin jirgin ruwa ya halaka mutum 27 a Gbajibo, karamar hukumar Kaiama a jihar Kwara, yayin dawowa daga kasuwa a Niger.
Primate Ayodele ya hango rikice-rikicen da za su fada wa gwamnonin jihohi 6, inda ya bukace su da su guji siyasar rikici, su mayar da hankali kan jin daɗin jama'a.
Ana yawan samun matsala tsakanin gwamnoni da mataimakansu wanda yana farawa ne daga zargi na rashin biyayya, shisshigi daga wasu ‘yan siyasa, ko rauni.
Gwamnatin Neja ta rufe ta rufe wani otel da aka mayar da shi gidan karuwai da wasu gidajen karuwai a kusa da wani masallacin Juma'a a karamar hukumar Mokwa.
Jagora a APC, Dr. Mohammed Santuraki ya zargi gwamnatin tarayya da nuna bangaranci ga Neja a nadin shugabannin Hukumar Raya Arewa ta Tsakiya (NCDC).
Dan majalisar wakilai daga jihar Neja, Hon Adamu Lokoja, ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC. Ya samu tarba daba shugabannin APC na jihar.
Jam'iyyar APC a jihar Neja ta kara ƙarfi da manyan kusoshin adawa ciki har da mutum 2 da suka nemi zama gwamna a 2023 suka baro jam'iyyunsu zuwa cikinta.
Mutane da dama sun rarrabu kan furucin Gwamnan Niger, Mohammed Umar Bago da ya janyo cece-kuce bayan shiga cikin cocin Living Faith a Minna da ke jihar.
Gwamnan Neja, Mohammed Umaru Bago ya bayyana akwai bukatar cure mutane daga ƙangin talauci da yaƙi da jahilci domin kawo ƙarshen matsalar tsaro a ƙasar nan.
Jihar Niger
Samu kari