An Dawo da Magana kan Bude Iyakoki bayan Farashin Abinci Ya Fara Sauka

An Dawo da Magana kan Bude Iyakoki bayan Farashin Abinci Ya Fara Sauka

  • Dr Mu’azu Babangida Aliyu ya kalubalanci rufe iyakokin Najeriya duk da ci gaba da fitar da kayayyaki da ake zuwa ƙasashen ECOWAS
  • Tsohon gwamnan ya yi kira da a mayar da hankali kan inganta ilimi a Arewa, yana cewa babu wata jiha da ke da kashi 50% na kwararrun malamai
  • Ya kuma yi nuni da buƙatar haɗin kai tsakanin sabuwar ma’aikatar ci gaban dabbobi da jami’o’i domin inganta aikin noma da kiwo

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Niger - Tsohon gwamnan jihar Neja, Dr Mu’azu Babangida Aliyu, ya bayyana damuwarsa kan rufe iyakokin Najeriya.

Dr Mu'azu Babangida ya koka yana mai tambayar amfani da wannan mataki yayin da kayayyakin Najeriya ke ci gaba da shiga ƙasashen ECOWAS ta barauniyar hanya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta ɓullo da sabon tsari, za ta riƙa biyan mutane kudi don su halarci makarantu 2

Mu'azu Babangida
Tsohon gwamnan Neja ya yi magana kan ilimi da rufe iyakokin Najeriya. Hoto: Niger State Government
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta wallafa cewa tsohon gwamnan ya ce lamarin yana kawo cikas ga tattalin arzikin Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me aka amfana da shi bayan rufe iyakoki?

Dr Mu’azu Babangida Aliyu ya tambayi mahimmancin rufe iyakokin Najeriya, yana mai cewa duk da matakin, kayayyakin ƙasar na cigaba da shiga ƙasashen ECOWAS kamar yadda aka saba.

A cewarsa;

“Fiye da rabin kayayyakin da ake samu a kasuwannin ECOWAS daga Najeriya ne.
"Duk da rufe iyakoki, har yanzu ana sayar da shanu a ƙasar Nijar da farashi mai rahusa fiye da Najeriya.”

Ya yi kira ga hukumomin gwamnati da su sake nazarin matakan da suke ɗauka domin tabbatar da cewa suna haifar da ci gaba maimakon haifar da ƙarin matsaloli.

Rashin kwararrun malamai a Arewa

A wani ɓangare na jawabin nasa, Dr Babangida Aliyu ya jaddada muhimmancin ilimi ga ci gaban al’umma, yana mai cewa yankin Arewa na fama da ƙarancin kwararrun malamai.

Kara karanta wannan

APC ta yi kaca kaca da Atiku Abubakar, ta fadi wanda ke haddasa rikici a PDP

“Babu wata jiha a Arewa da ke da kashi 50% na kwararrun malamai. Yakamata gwamnati ta haɗa hannu da jami’o’i domin samar da horo ga malamai da manoma,”

- Dr Mu'azu Babangida Aliyu

Ya kuma nuna damuwa kan yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a yankin, yana mai cewa wannan na iya ci gaba da haifar da talauci da koma baya.

Rashin kayayyakin aikin noma

A lokacin taron, shugabar wani kamfanin tumatur a Jos, Mira Mehta ta ce matsalolin da ake fuskanta wajen samar da kayayyakin noma a Najeriya suna haifar da tsadar kayan masarufi.

Mira Mehta ta ce;

“Kasarmu tana shigo da sama da kashi 30% na abincin da muke ci, kuma wannan yana shafar tattalin arziki saboda ana buƙatar amfani da Dala wajen shigo da kayan.”

Haka zalika, ta bayyana cewa rashin ingantaccen tsari da tsadar kayan aiki suna hana masana’antun Najeriya yin gasa da ƙasashen waje wajen samar da kayayyaki.

Kara karanta wannan

IPOB ta sako Sheikh Gumi a gaba bayan shawarsa a kan ta'addanci

Kira ga hadin kai domin cigaba

Dr Mu’azu Babangida Aliyu ya yi kira ga sabuwar ma’aikatar ci gaban dabbobi da jami’o’i da su haɗa kai domin samar da horo ga manoma a fannin kiwo da noma.

Daily Trust ta wallafa cewa tsohon gwamnan ya ce;

“Muna buƙatar ilimi domin samun mutane da za su himmatu wajen yin abubuwan da ke da mahimmanci ga ci gaban al’umma.”

Hakazalika, ya yi kira ga shugabanni da su duba hanyoyin da za su rage tsadar kayan masarufi da kuma tabbatar da cewa mutane suna samun abinci mai sauƙi da arha.

Za a inganta noma a jihar Nasarawa

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Nasarawa ya fitar da tsarin habaka noma da kayan zamani a jihar.

Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana haka ne yayin wata ziyara da ya kai kasar China da kuma neman hada kai da masana domin bunkasa noma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng