Agaie: Babban Limami Ya Rasu a Jihar Neja, Gwamna da Jama'a Sun Girgiza
- Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya yi alhini kan rasuwar Babban Limamin Agaie, Sheikh Muhammadu Kudu
- Mohammed Umaru Bago ya bayyana rasuwar limamin a matsayin babban rashi ga mutanen Agaie da Jihar Neja baki daya
- Jama’a da dama sun yi addu’ar neman gafara da fatan samun aljanna ga marigayin a shafukan sada zumunta bayan sanar da rasuwarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Niger - Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya nuna alhininsa kan rasuwar babban limamin Agaie, Sheikh Muhammadu Kudu.
Ta hannun mai magana da yawunsa, Bologi Ibrahim, gwamnan ya aika ta’aziyyarsa ga Sarkin Agaie, Alhaji Yusuf Nuhu, da mambobin Majalisar Masarautar Agaie.

Asali: Facebook
Haka zalika, Bologi Ibrahim ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa gwamna Bago ya yi ta'aziyya ga iyalai da dangin marigayin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya bayyana cewa wannan rashin ba mutanen Agaie kawai ya girgiza ba, har ma da daukacin Jihar Neja.
Umaru Bago fadi haka ne lura da ganin irin gagarumar gudunmawar da marigayin ya bayar a harkokin zaman lafiya da ci gaban addinin Musulunci.
Gudunmawar marigayi Sheikh Kudu
A cewar Gwamna Umaru Bago, Sheikh Muhammadu Kudu Agaie ya kasance jagora mai kishin addini.
Gwamnan ya kara da cewa malamin ya yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban addinin Musulunci a Masarautar Agaie.
Umaru Bago ya ce;
“Rasuwar Sheikh Muhammadu Kudu babban rashi ne da ba za a manta da irin gudunmawar da ya bayar wajen kyautata rayuwar jama’a ba.”
Gwamnan ya jaddada cewa al’ummar Agaie za su ci gaba da tuna marigayin bisa kyawawan halayensa da sadaukarwar da ya yi wajen inganta zamantakewa da addini.
Addu’o’in da alhini ga iyalan malamin
Gwamnan ya yi addu’ar Allah Ya gafarta wa Sheikh Muhammadu Kudu kura-kuransa, Ya kuma sanya shi cikin aljanna madaukakiya.
Hakazalika, ya roki Allah Ya ba Sarkin Agaie, mambobin majalisar masarauta, iyalan mamacin, da daukacin al’ummar Agaie hakurin jure wannan babban rashi.
Gwamnan ya ce;
“Mun yi babban rashi amma za mu ci gaba da jurewa tare da yin addu’a domin nema wa marigayin lada da gafara.”
Addu'ar Jama’a a shafukan sada zumunta
Bayan sanarwar rasuwar Sheikh Muhammadu Kudu, jama’a da dama sun nuna alhinin su a shafukan sada zumunta, suna mai fatan Allah Ya gafarta wa mamacin.
Addu’o’i da kalaman ta’aziyya sun cika wurare irin su Facebook, inda mutane ke bayyana soyayya da godiya ga marigayin bisa gudunmawar da ya bayar ga al’umma.
Rasuwar Sheikh Muhammadu Kudu Agaie ta bar babban gibi ga Masarautar Agaie da Jihar Neja baki daya.
Farfesa dan shekaru 59 ya haddace Kur'ani
A wani rahoton, kun ji cewa wani Farfesa a jami'ar jihar Legas ya haddace Kur'ani mai girma bayan shafe shekaru yana kokari.
Legit ta ruwaito cewa Farfesa Tajudden Yusuf ya haddace Kur'ani ne yayin da ya cika shekaru 59 da haihuwa wanda hakan ya nuna naci da ya sanya.
Asali: Legit.ng