'An Rasa Rayuka': An Shiga Tashin Hankali a Neja da Nakiya Ta Tarwatse a Wani Gida
- Wani abin fashewa ya tarwatse a wurin hakar ma’adanai a Sabon Pegi, karamar hukumar Mashegu, lamarin da ya jawo rasa rayuka
- Rundunar ‘yan sanda ta ce fashewar na da alaƙa da tarwatsewar nakiya da aka ajiye a wani gidan zama don ayyukan hakar ma’adanai
- Sarkin yankin, Muhammad Baiwa, ya yi kira da a kwantar da hankali tare da neman a ladabtar da masu ajiye nakiya a gidajensu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Neja - Kwanaki kaɗan bayan fashewar tankar mai a Dikko, karamar hukumar Gurara, wacce ta halaka fiye da mutane 100, wata annobar ta sake afkuwa a Neja.
Tarwatsewar wani abin fashewa mai tsanani ya afku a wurin hakar ma’adanai a Sabon Pegi, karamar hukumar Mashegu, a safiyar Lahadi.

Asali: Facebook
Fashewar nakiya ta kashe mutane 6
Rahotannin farko sun nuna fashewar na da alaƙa da rashin kyakkyawan sarrafa kayan fashewa da ake amfani da su wajen hakar ma’adanai, inji rahoton Channels.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan fashewa ta yi sanadiyyar mutuwar mutum hudu tare da raunata wasu da dama, kamar yadda mazauna garin Sabon Pegi suka shaida.
Shaidu sun ce fashewar ta girgiza yankin Sabon Pegi da kewaye, ciki har da New Bussa, inda jama’a suka tsere zuwa daji saboda tsoro.
Neja: 'Yan sanda sun fitar da rahoton farko
Sai dai, rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta fitar da wata sanarwa daban, inda ta ce fashewar ta auku ne sakamakon ajiyar nakiya.
A cewar kakakin 'yan sandan, SP Wasiu Abiodun, nakiyar da wani Yushau ya ajiye a gidansa don ayyukan hakar ma’adanai ce ta fashe.
Wata mata mai suna Fatima Sadauki ta mutu, yayin da mutane shida suka ji raunuka, kuma suna karɓar magani a Asibitin Kainji, New Bussa.
Wanda ake zargi ya tsere bayan fashewar nakiyar
Fashewar ta lalata gidaje 12, kuma ana ci gaba da aikin ceto yayin da ake fargabar akwai wasu da suka makale a ƙarƙashin baraguzan gidaje.
Rahotanni sun nuna cewa an ajiye nakiyar ne a wani gida kusa da wurin hakar ma’adanai, inda wannan wurin ya lalace gaba ɗaya.
Yushau wanda ake zargin shi ne ya jawo fashewar nakiyar, ya tsere kuma ba a san inda yake ba amma 'yan sanda sun ce suna ci gaba da bincike.
Sarkin yankin, Muhammad Baiwa, ya yi kira da a kwantar da hankali tare da ladabtar da masu ajiye nakiya a gidajen zamansu.
Bam ya tarwatse a makarantar Islamiyya
A wani labarin, mun ruwaito cewa dalibai biyu sun rasa rayukansu sakamakon fashewar wani abu a makarantar Islamiyya da ke ƙaramar hukumar Bwari, Abuja.
Wata majiya ta bayyana cewa ana zargin sabon ɗalibi ya kawo abin fashewar da ake tunanin bam ne, wanda ya jikkata ɗalibai da dama.
Ko da yake babu wata sanarwa daga ƴan sanda a hukumance, rahotanni sun nuna cewa jami'an tsaro sun isa makarantar kuma sun fara bincike kan lamarin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng