Masu Garkuwa Da Mutane
An gargadi Shugaban kasa Bola Tinubu kan tashin hankalin da zai dabaibaye gwamnatinsa a sabon hasashen da Primate Elijah Ayodele ya saki bayan sace shugaban PDP.
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya gargadi shugabannin kananan hukumomin Abuja kan gaza halartar taron tsaro na wata wata da ake yi a majalisar kananan hukumomin Abuja.
Rundunar ƴan sanda ta musamman da IGP ya kafa da kuma dakarun hukumar ƴan sandan Abuja sun sheƙe wani ɗan bindiga da aka jima ana nema ruwa a jallo a Bwari.
Dakarun yan sanda da haɗin guiwar mafarauta sun yi nasarar sheke masu garkuwa 3 yayin da suka yi yunkurin sace wasu mutum biyu a jihar Adamawa jiya Laraba.
Wani DPO na ‘yan sanda ya ki amincewa da karbar cin hancin naira miliyan daya da wani dan bindiga ya ba shi bayan an kama shi a wani otal da ke garin Kaduna.
Jami'an sashin yaƙi da garkuwa da mutane na rundunar yan sandan Abuja sun samu nasarar ceto mutane 14 da aka yi garkuwa da su, sun sheƙe mutum ɗaya.
Gawurtaccen mai garkuwa da mutane a birnin tarayya Abuja, ya musanta ƙaifin da yan sanda suke tuhumarsa da shi. Ya ce shi dan fanshi da makami ne.
Wasu gwamnoni akalla 9 a Najeriya sun tabbatar da aniyarsu ta zartar da hukuncin kisa ko ɗaurin rai da rai kan duk wanda aka kama da laifin garkuwa da mutane.
Rundunar 'yan sanda ta kama Mansir Hassan, wanda ke yi wa 'yan ta'adda safarar makamai a dajin Zurmi, jihar Zamfara. An kama shi ne a yankin Zariya a kan babur.
Masu Garkuwa Da Mutane
Samu kari