Yan Sanda Sun Dakile Harin Yan Bindiga, Sun Ceto Mutanen da Aka Yi Yunkurin Sacewa

Yan Sanda Sun Dakile Harin Yan Bindiga, Sun Ceto Mutanen da Aka Yi Yunkurin Sacewa

  • Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta samu nasarar ceto wasu mutum biyu mata da miji da ƴan bindiga suka yi yunƙurin yin garkuwa da su
  • Jami'an rundunar ƴan sandan sun samu wannan nasarar ne bayan sun samu kiran gaggawa kan shirin ƴan bindiga
  • Bayan fattakar ƴan bindigan, ƴan bindigan sun sada matar da ƴan uwanta yayin da aka kai mijin asibiti saboda raunukan da ya samu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce ta daƙile wani yunƙurin yin garkuwa da wani mutum da matarsa ​​a yankin Rigasa da ke ƙaramar hukumar Igabi a jihar.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar, ASP Mansir Hassan ya tabbatar faruwar lamarin jiya Asabar a Kaduna, cewar rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun halaka abokan juna a wani sabon hari a Nasarawa

Yan sanda sun ceto mutum biyu a Kaduna
Yan sanda sun ceto mata da miji da aka yi yunkurin sacewa a Kaduna Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Ya ce jami’an rundunar sun ceto ma’auratan ne da misalin ƙarfe 2:05 na daren ranar Asabar, 30 ga watan Disamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hassan ya ce jami’an da ke sintiri sun daƙile yunkurin yin garkuwa da mutanen ne a tsakanin tashar jirgin ƙasa zuwa mahadar Mando da ƙauyen Mahuta na Igabi, rahoton PM News ya tabbatar.

Yadda aka ceto ma'auratan

A kalamansa:

"Da misalin ƙarfe 2:05, jami’an mu sun samu kiran gaggawa cewa wasu ƴan bindiga sun kai farmaki wani gida."
"Ba tare da ɓata lokaci ba jami'an ƴan sanda suka garzaya yankin suka mamaye yankin baki ɗaya, sakamakon haka ƴan bindigar suka gudu suka bar mutanen da suka ɗauka."
"Mijin da aka ceto ya samu raunuka a kafadarsa da kansa amma an garzaya da shi asibitin tunawa da Yusuf Dantsoho domin kula da lafiyarsa."

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun tafka ta'asa a Abuja, sun sace babban basarake da wasu mutum 5

Ya kuma ƙara da cewa tuni aka haɗa matar da ƴan uwanta, sannan jami'an ƴan sanda sun zafafa sintiri domin kamo masu laifin.

Yayin da yake nanata ƙudurin rundunar na kawar da miyagun laifuka a jihar, Hassan ya buƙaci mazauna yankin da su bayar da sahihin bayanai ga ƴan sanda da sauran hukumomin tsaro.

Ƴan Sanda Sun Cafke Mai Garkuwa da Ƙananan Yara

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an rundunar ƴan sandan jihar Ogun sun cafke wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne kuma mai safarar ƙananan yara, mai suna Tayo Adeleke.

Adeleke ya ƙware wajen yin garkuwa da mutane da sayar da yara ga masu saye a Jamhuriyar Benin da ke makwabtaka da Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel