Yan Bindiga Sun Shiga Har Fada Sun Yi Awon Gaba da Babban Basarake

Yan Bindiga Sun Shiga Har Fada Sun Yi Awon Gaba da Babban Basarake

  • Miyagun ƴan bindiga sun tafka sabuwar ta'asa a wani hari da suka kai fadar babban basarake a jihar Imo
  • Ƴan bindigan sun yi awon gaba da tsohon shugaban majalisar sarakunan jihar Imo, mai martaba Eze Samuel tare da ɗan'uwansa
  • Shaidun ganau ba jiyau ba sun tabbatar da cewa ƴan bindigan sun yi awon gaba da mutanen ne a harabar gidan basaraken

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Owerri, jihar Imo- Wasu ƴan bindiga da ba a san ko su waye ba a safiyar ranar Asabar sun yi garkuwa da tsohon shugaban majalisar sarakunan jihar Imo kuma Sarkin Orodo, Mai Martaba, Eze Samuel Agunwa Ohiri.

An tattaro daga wani ganau cewa lamarin ya faru ne a ƙofar gidan Ohiri da ke Orodo, ƙaramar hukumar Mbaitoli a jihar Imo, da misalin ƙarfe 08:30 na safe, cewar rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun sheke yan ta'adda 10, sun ceto mutanen da suka sace

Yan bindiga sun sace basarake a Imo
Yan bindiga sun sace babban basarake a Imo Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Har ila yau, shaidar ganau ɗin wanda ya bayar da labarin, ya yi iƙirarin cewa an kuma yi garkuwa da ɗan uwan ​​Ohiri wanda ɗan kasuwa ne da ke zaune a Amurka, mai suna Solomon Ohiri, rahoton TheCable ya tabbatar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindigan suka sace basaraken

Game da yadda lamarin ya faru, ganau ɗin ya bayyana cewa:

“A safiyar yau Asabar, Ohiri da ɗan’uwansa daga Amurka, sun yanke shawarar fita da motarsu a cikin shagalin bikin Kirsimeti domin ziyartar wasu abokansu. Bayan ziyarar su ne suka dawo.
"Yayin da suka isa harabar gidan Ohiri, sun ajiye motarsu a gefe guda na harabar gidan, yayin da su biyun suke ta tattaunawa ta ƙarshe kafin su yi sallama da juna. Wata mota ƙirar Highlander cike da ƴan bindiga ta iso suna ta harbe-harbe. Sun ɗauke su zuwa cikin motar. Sun doshi hanyar Njaba zuwa Orlu."

Kara karanta wannan

Wasu mata sun fito zanga-zanga a fusace, sun banka wa gidan basarake wuta a Bokkos

Sai dai kuma wani shaidar ganau ɗin, ya yi iƙirarin cewa ɗan’uwan Ohiri, Solomon, ya tsero daga hannun ƴan bindigan.

Ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Imo ba, Henry Okoye, zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Ƴan Bindiga Sun Sace Mata da Miji

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun sace wata mata da mijinta tare da ƙaramin yaro a jihar Neja.

Ƴan bindigan masu yawan gaske sun tafka wannan ta'asar ne a ƙauyen Garam wanda ke makwabtaka da birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel