Yan Sanda Sun Kama Mai Garkuwa da Mutane da Ke Sayar da Yara

Yan Sanda Sun Kama Mai Garkuwa da Mutane da Ke Sayar da Yara

  • Dubun wani mai garkuwa da mutane tare da safarar ƙananan yara yana sayar wa a jihar Ogun ta cika
  • Jami'an rundunar ƴan sandan jihar tare haɗin gwiwar ƴan banga sun yi nasarar cafke mai laifin a ƙauyen Omu Pempe
  • Binciken da aka gudanar ya nuna cewa mai laifin suna ƙungiya wacce suke sace yara tare da sayar da su a Jamhuriyar Benin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ogun - Jami'an rundunar ƴan sandan jihar Ogun sun cafke wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne kuma mai safarar ƙananan yara, mai suna Tayo Adeleke.

Adeleke ya ƙware wajen yin garkuwa da mutane da sayar da yara ga masu saye a Jamhuriyar Benin da ke makwabtaka da Najeriya.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun sheke miyagun yan bindiga 6 a jihar Bauchi

An cafke mai garkuwa da mutane a Ogun
Mai garkuwa da yara ya fada komar yan sanda a Ogun Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Adeleke yana tsare a hannun ƴan sanda, inda ake masa tambayoyi kan yunƙurin da ya yi da wasu mutum biyu, waɗanda a halin yanzu suka tsere na sace yara a ƙauyen Omu Pempe da ke ƙaramar hukumar Obafemi-Owode a jihar Ogun ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka cafke mai garkuwa da mutanen

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa wadanda ake zargin sun dira ne a cocin Baptist da ke Omu Pempe da misalin ƙarfe 2:00 na rana a kan babur.

Manufar su ita ce su kwashe yara daga cocin su sayar da su a Jamhuriyar Benin.

Sai dai jami'an tsaro na So-Safe Corps sun samu kiran gaggawa kan yunƙurin mutanen, inda suka sanar da jami’in ƴan sanda na yankin.

Lokacin da aka ƙalubalanci mutanen uku game da abin da ya kai su ƙauyen, ba su iya ba da wani cikakken bayani ba, sannan suka yi yunƙurin guduwa.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da jami'in dan sanda ya rasa ransa a hannun budurwarsa, an fdi abin da ya faru

Wane bayani ƴan sanda suka yi?

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Omolola Odutola, yayin da take tabbatar da faruwar lamarin, ta bayyana cewa an kama Adeleke ne tare da haɗin gwiwar ƴan sanda da jami'an tsaro na So-Safe Corps da sauran ƴan banga a yankin.

A cewar Odutola, wanda ake zargin ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi a lokacin da ake masa tambayoyi, rahoton The Guardian ya tabbatar.

Ta ce ya bayyana cewa sun je ƙauyen ne domin satar yara, kuma suna da ƙungiya wacce suka shahara wajen sace ƙananan yara inda suke sayar da su a Jamhuriyar Benin.

"Mun kama dlɗaya kuma zai taimaka wajen cafke sauran." A cewarta.

Ƴan Sanda Sun Sheƙe Ƴan Bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Bauchi ta sheƙe wasu miyagun ƴan bindiga shida a jihar.

Jami'an rundunar sun kuma ƙwato kayayyaki masu yawa da suka haɗa da makamai da wayoyi a hannun ƴan bindigan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel