Kano: An Kama Wani Matashin Da Ya Sace Yaro Dan Shekara 3, An Gano Alakarsu

Kano: An Kama Wani Matashin Da Ya Sace Yaro Dan Shekara 3, An Gano Alakarsu

  • Daga jihar Kano, rundunar 'yan sandan jihar Kano ta cafke wani Salisu Adamu da laifin yin garkuwa da yaro dan shekara uku
  • Rahotanni sun bayyana cewa, yaron mai suna Auwalu Aminu dan uwane ga Salisu, amma ya yi garkuwa da shi don neman kudin fansa
  • Da 'yan sanda suka tuhume shi, Salisu ya amsa laifin, inda ya ce ya so yin amfani da kudin don biyan basussukan da ake binsa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kano - Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da cafke wani matashi mai suna Salisu Adamu dan shekara 18 daga Danbatta Kano.

Rundunar ta kama Adamu bisa zarginsa da kitsa sace wani dan uwansa Auwalu Aminu mai shekaru uku da haihuwa.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe yan sanda, sun sace fasinjojin da suka tafi hutun Kirsimeti

Matashi ya yi garkuwa da yaro dan shekara 3 a Kano
Rundunar 'yan sanda ta kama Adamu bisa zarginsa da kitsa sace wani dan uwansa Auwalu Aminu mai shekaru uku da haihuwa. Hoto: @KanoPoliceNG, @LeadershipNGA
Asali: Facebook

Mallam Aminu ya shigar da karar batan yaronsa Auwalu

Mahaifin yaron, Malam Aminu Garba Danbatta ne ya shigar da rahoton faruwar lamarin a ofishin ‘yan sanda a ranar 19 ga Disamba, 2023, Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwanaki biyar da bacewar yaron, Adamu ya tuntubi iyalan da boyayyar lamba, inda ya bukaci a biya sa kudin fansa naira miliyan daya domin ya sako Auwalu lafiya.

Daga nan ne kwamishinan ‘yan sanda, CP Muhammed Usaini Gumel, ya ba ‘yan sanda umurnin tsaurara binciken lamarin.

Bayan gudanar da bincike ne 'yan sandan suka cafke Adamu tare da ceto yaron a karamar hukumar Gwale ta jihar Kano.

Salisu Adamu ya amsa laifin satar Auwalu, ya fadi dalili

A yayin da ake yi masa tambayoyi, Adamu ya amsa aikata laifin shi kadai, inda ya ce matsalar kudi ce ta sa shi ya yi hakan.

Kara karanta wannan

Jerin abubuwa 5 muhimmai da ya kamata Ku sani game da marigayi Ghali Umar Na'Abba

Ya ce ya shirya yin amfani da kudin fansar ne wajen warware basussukan da ake binsa da suka haura Naira 100,000.

Danbatta ya bayyana kaduwarsa da takaicin yadda ya gano cewa wani dan uwa ne ya yi garkuwa da dan shi.

CP Gumel ya baiwa jama’a tabbacin gudanar da cikakken bincike, inda ya yi alkawarin cewa Adamu zai fuskanci hukuncin shari’a.

Rikakken dan daba da ake nema ruwa a jallo ya mika wuya a jihar Kano

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito maku yadda mahaifiyar wani rikakken dan daba ta mika shi hannun 'yan sanda a Kano, tare da nema masa afuwa.

Dan dabar da ake kira 'Hantar Daba' ya kasance a jerin masu laifin da 'yan sanda suka saka kudi ga duk wanda ya gano inda suke, saboda laifukan daba a fadin jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel