Tashin Hankali Yayin Da ’Yan Bindiga Suka Yi Awon Gaba da Shugaban Karamar Hukuma a Jihar Arewa
- Wasu 'yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da shugaban karamar hukumar Akwanga, jihar Nasarawa
- An yi garkuwa da Safiyanu Isa Andaha tare da wani Alhaji Adamu a yammacin ranar 1 ga Janairu, 2024 a hanyar Akwanga-Andaha
- Tuni jami'an 'yan sanda da hadin guiwar wasu jami'an tsaro suka fita farautar 'yan bindigar don kubutar da mutanen da suka kama
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Nasarawa - Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban karamar hukumar Akwanga a jihar Nasarawa, Safiyanu Isa Andaha.
Mai baiwa gwamnan jihar Nasarawa shawara kan harkokin kananan hukumomi da masarautu, Mista Haruna Kassimu, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Asali: Twitter
Abin da 'yan sanda suka ce kan sace Safiyanu Isa
Kassimu ya ce an sace Safiyanu Isa ne a kauyen Ningo da ke karamar hukumar Akwanga ta jihar tare da wani Alhaji Adamu Custom a yammacin ranar 1 ga Janairu, 2024, rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kara da cewa jami’an tsaro sun kai dauki cikin gaggawa ta hanyar bin bayan ‘yan bindigar da suka gudu tare da shugaban karamar hukumar, sai dai ba a san inda suka kai su ba.
A cewar Tribune Online, kakakin ‘yan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel, ya ce jami’an tsaro na nan suna kokarin ganin an sako shugaban karamar hukumar da sauran wanda aka kama.
Sokoto: Gwamna Ahmed Aliyu ya kaddamar da rundunar tsaro
A wani labarin, gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya kaddamar da rundunar tsaron jihar da nufin taimakawa sauran jami'an tsaro wajen magance matsalar tsaro a jihar.
Sai dai gwamnan ya ce bai samar da rundunar tsaron don ta zama kishiyar rundunar 'yan sanda ba, kawai dai ya yi hakan don karfafa tsaro a jiharsa.
Asali: Legit.ng