Yadda makiyaya suka tarwatsa kasuwar mako yayin da suke fada kan budurwa a wata jahar arewa

Yadda makiyaya suka tarwatsa kasuwar mako yayin da suke fada kan budurwa a wata jahar arewa

  • An yi arangama tsakanin kungiyoyin makiyaya biyu bayan waninsu ya kwacewa abokin hamayya budurwa
  • Lamarin wanda ya afku a ranar Juma'a ya yi sanadiyar tarwatsa kasuwar mako da ake ci a garin Tegina da ke karamar hukumar Rafi ta jihar Neja
  • Yan kasuwa sun tsere sun bar kayayyakinsu domin duk a tunaninsu yan bindiga ne suka kawo farmaki

Niger - Wasu makiyaya a ranar Juma’a sun tarwatsa kasuwar mako da ake ci a garin Tegina da ke karamar hukumar Rafi ta jihar Neja yayin da suke fada a kan budurwa.

Yan kasuwa da dama da abokan cinikinsu sun tsere don tsira da rayuwarsu, inda suka bar kayayyaki da sauran abubuwa masu muhimmanci.

Jama’a sun tsorata sosai domin a tunanin su yan bindiga ne suka farmaki kasuwar bayan arangama tsakanin kungiyoyin na makiyaya, Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai sabon hari jihar shugaban ƙasa ana ruwan sama, sun aikata ɓarna

Niger
Yadda makiyaya suka tarwatsa kasuwar mako yayin da suke fada kan budurwa a wata jahar arewa Hoto: Vanguard
Asali: UGC

A garin Tegina ne yan bindiga suka sace yaran makarantar Islamiyya 136 a ranar 30 ga watan Mayu sannan aka sake su a ranar 26 ga watan Agustan 2021 bayan iyayensu sun biya kudin fansa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai dai kuma, sabanin fargabar da yan kasuwa da abokan cinikinsu suka shiga a kasuwar makon, makiyayan na gudanar da taron al’ada da suka saba ne a yayin bikin Sallah inda makiyaya kan hadu da yawansu tare da yan matansu a kasuwa don siyan abubuwa da shakatawa.

A yayin wannan biki ne, wani makiyayi daga wata kungiya daban ya kwacewa wani abokin hamayya budurwarsa lamarin da ya yi sanadiyar barkewar rikici a tsakanin magoya bayan kungiyoyin.

Fadan ya kan fara ne daga mutumin da aka kwacewa budurwa.

Rahoton ya kuma kawo cewa wani mazaunin yankin, Hassan Muhammad, ya ce sai da jami’an yan sanda da ke wajen suka shiga tsakani ta hanyar yin kame-kame kafin zaman lafiya ya dawo kasuwar.

Kara karanta wannan

Fashin magarƙama: An kama wani fursuna da ya tsere daga gidan Yarin Kuje ɗauke da kayan laifi a Katsina

Muhammad ya ce yan sandan sun yi harbe-harbe a iska don tsoratawa da kuma tarwatsa masu fadan.

Ya kuma ce makiyayan da suka jikkata a rikicin na samun kulawa a asibitoci masu zaman kansu da ke yankin.

Sai dai ba a samu jin ta bakin kakakin yan sandan jihar, Wasiu Abiodun ba a kan lamarin.

Dakarun sojoji sun dakile harin ta’addanci kan sansaninsu a jihar Neja

A wani labarin kuma, dakarun sojoji sun dakile harin da wasu yan ta’adda da ake zaton suna da alaka da yan Boko Haram/ISWAP suka yi yunkurin kaiwa sansaninsu a Sarkin Pawa, hedkwatar karamar hukumar Munya ta jihar Neja.

Yan ta’addan wadanda suka so kaiwa sojojin harin bazata sun isa yankin ne da sanyin safiyar Litinin, 18 ga watan Yuli, sai dai kuma jami’an tsaron sun zama cikin shiri inda suka nuna turjiya, Channels Tv ta rahoto.

Da yake tabbatar da harin a yau Litinin, kakakin gamayyar kungiyoyin Shiroro (COSA), Salis Sabo, ya bayyana cewa daruruwan ‘yan ta’addan sun zo yankin sannan suka yi kokarin tarwatsa sansanin sojojin.

Kara karanta wannan

Hotuna: Yadda Sadiq Ango ya canza kamanni bayan yin wata 3 hannun 'yan bindiga

Asali: Legit.ng

Online view pixel