Yanzu Yanzu: An tsige mataimakin gwamnan jihar Oyo daga kan kujerarsa

Yanzu Yanzu: An tsige mataimakin gwamnan jihar Oyo daga kan kujerarsa

  • Majalisar dokokin jihar Oyo ta tsige mataimakin gwamnan jihar Mista Rauf Olaniyan, daga kan kujerarsa
  • Kamar yadda shugaban masu rinjaye a majalisar, Sanjo Adedoyin, ya bayyana, an samu Olaniyan da dukka laifukan da ake tuhumarsa a kai
  • An sauke mataimakin gwamnan daga kujerar tasa ne a zaman majalisa na yau Litinin, 18 ga watan Yuli

Rahotanni da ke zuwa mana sun kawo cewa an tsige mataimakin gwamnan jihar Oyo, Mista Rauf Olaniyan, daga kan kujerarsa.

Nigerian Tribune ta rahoto cewa an tsige Olaniyan ne bayan majalisar dokokin jihar ta amince da rahoton kwamitin mutum bakwai da babban alkalin kotu ya kafa don binciken zargin da ake yiwa mataimakin gwamnan na rashin da’a a zamanta na ranar Litinin.

Rauf Olaniyan
Yanzu Yanzu: An tsige mataimakin gwamnan jihar Oyo daga kan kujerarsa Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar Oyo, Sanjo Adedoyin, ya ce an samu mataimakin gwamnan da dukka laifukan da ake zarginsa a kai.

Kara karanta wannan

Gwamna ya sallami baki ɗaya hadimansa daga kan kujerunsu saboda abu ɗaya

Majalisar ta Oyo ta ce tsige Olaniyan daga kujerarsa ya yi daidai da sashi na 188(9) na kundin tsarin mulki na 1999 (kamar yadda aka gyara), jaridar Guardian ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shirin tsige shi: Mataimakin gwamnan Oyo ya maka majalisar dokoki a Kotu

A baya mun kawo cewa mataimakin gwamnan jihar Oyo, Injiniya Rauf Olaniyan, ya nufi babbar Kotun jiha da nufin ta dakatar da shirin tsige shi da majalisar dokokin jihar ke yi.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mambobi 24 cikin 32 na majalisar dokokin sun zargi mataimakin gwamnan, a cikin korafin, da, "Rashin ɗa'a, cin nutuncin Ofis, karkatar da kuɗi, rashin zuwa aiki, rashin biyayya da sauran su."

Rahoto ya nuna cewa mataimakin gwamnan ya yi jawabi dalla-dalla kan dukkan zargin da majalisa ke masa ta bakin lauyan sa Afolabi Fashanu, SAN.

Kara karanta wannan

Fannin ilimi: Wata kungiyar agaji ta Saudiyya za ta kafa jami'ar Musulunci a Zamfara

Asali: Legit.ng

Online view pixel