Guguwar iska ta kashe mutane 6 tare da jikkata wasu 65 a jihar Jigawa
- Guguwar iska ta yi sanadiyar rasa rayukan mutane shida a yankin karamar hukumar Kafinhausa da ke jihar Jigawa
- Mutane 65 da suka jikkata sakamakon annobar na nan kwance a babbar asibitin gwamnati da ke yankin
- Lamarin wanda ya afku a ranar Talata ya maida mutane da dama marasa galihu sakamakon lalata gidaje da annobar ta yi
Jigawa - Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Jigawa (SEMA) ta ce mutane shida sun mutu sakamakon guguwar iska da ta lalata gidaje a karamar hukumar Kafinhausa da ke jihar.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa babban sakataren hukumar, Yusuf Sani, ya ce lamarin ya afku ne a ranar Talata.
A yan baya-bayan nan, garuruwa da dama a Najeriya sun fuskanci ambaliyar ruwa da guguwar iska, wanda ya lalata gidaje sannan ya mayar da mutane da dama marasa galihu.
Da yake magana kan lamarin na Jigawa, Sani ya ce mazauna yankin 65 ne suka jikkata a yayin guguwar iskar, inda ya kara da cewar an kwashe su zuwa babban asibitin gwamnati da ke yankin Kafinhausa na jihar, jaridar The Cable ta rahoto.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sani ya ce:
“Mutane shida sun rasa rayukansu yayin da wasu 65 da suka jikkata a sakamakon annobar suke kwance a asibiti.
“Jami’anmu da na hukumar bayar da agajin gaggawa ta tarayya (NEMA) suna a yankin don ganin matakin da barnar ya kai.”
Babban sakataren ya ce mutane da dama da suka rasa muhallinsu sakamakon lamarin suna samun mafaka a gidajen yan uwansu.
Ya kara da cewar a yanzu haka hukumar na duba matakin barnar da annobar ta yi kuma suna aiki don samar da wurin zama na wucin gadi ga mutanen da lamarin ya ritsa da su.
Hakazalika da yake martani kan lamarin, jami’in labarai da ke kula da yankin, Muhammad Umar, ya ce shugaban yankin, Muhammad Saminu ya ziyarci wadanda ke kwance a asibiti, jaridar Daily Nigerian ta rahoto.
Harin gidan yarin Kuje: Yan sanda sun kama wani fursuna da ya tsere a jihar Ogun
A wani labari na daban, rundunar yan sanda a Ogun a ranar Laraba, 13 ga watan Yuli, ta bayyana cewa ta kama wani da ya tsere daga gidan yarin Kuje, Yakubu Abdulmumuni, a yankin Sango-Ota da ke jihar.
Kakakin yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, a cikin wata sanarwa da manema labarai a Ota, ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar Litinin, jaridar Premium Times ta rahoto.
Asali: Legit.ng