Harin gidan yarin Kuje: Yan sanda sun kama wani fursuna da ya tsere a jihar Ogun

Harin gidan yarin Kuje: Yan sanda sun kama wani fursuna da ya tsere a jihar Ogun

  • Yakubu Abdulmumuni, wani fursuna da ya tsere yayin da yan bindiga suka farmaki magarkamar Kuje ya sake shiga hannu
  • Jami'an rundunar yan sandan Ogun sun kama Abdulmumuni a yankin Sango-Ota da ke jihar bayan samun bayanai cewa an gano shi yana yawo a yankin
  • Babbar kotun jihar Kogi ce ta tura wanda ake zargin magarkamar ta Kuje bisa kama shi da laifin hada kai da kuma aikata kisan kai

Ogun - Rundunar yan sanda a Ogun a ranar Laraba, 13 ga watan Yuli, ta bayyana cewa ta kama wani da ya tsere daga gidan yarin Kuje, Yakubu Abdulmumuni, a yankin Sango-Ota da ke jihar.

Kakakin yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, a cikin wata sanarwa da manema labarai a Ota, ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar Litinin, jaridar Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan Sanda Sunyi Nasarar Cafke Daya Cikin Yan Boko Haram Da Suka Tsere Daga Gidan Yarin Kuje

Gidan gyara halin Kuje
Harin gidan yarin Kuje: Yan sanda sun kama wani fursuna da ya tsere a jihar Ogun Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Mista Oyeyemi ya yi bayanin cewa an kama Abdulmumuni mai shekaru 28 ne bayan bayanai da jami’an yan sanda a hedkwatar rundunar da ke Sango-Ota, suka samu cewa an gano fursunan a yankin.

Ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Da samun labarin, sai shugaban yan sanda reshen Sango-Ota, SP Saleh Dahiru, ya gaggauta tara jami’ansa sannan ya tura su yankin inda aka kamo fursunan.
“Fusunan ya bayyanawa yan sandan cewa ya tsere ne daga gidan gyara hali na Kuje a ranar 5 ga watan Yuli, lokacin da yan bindiga suka farmaki magarkaman.
“Abdulmumuni ya kuma bayyana cewa babban kotun jihar Kogi ce ta yanke masa hukunci kan laifin hada baki da kuma kisan kai, sannan aka tura shi gidan yarin Kuje."

Ya bayyana cewa kwamishinan yan sanda a jihar, Lanre Bankole, ya umurci sashin binciken laifuka da su tura fursunan gidan gyara hali ba tare da bata lokaci ba, rahoton PM News.

Kara karanta wannan

Fashin magarkamar Kuje: FG ta fitar da bayanan 'yan Boko Haram din da suka tsere

Yan Sanda Sunyi Nasarar Cafke Daya Cikin Yan Boko Haram Da Suka Tsere Daga Gidan Yarin Kuje

A wani lamari makamancin wannan, biyo bayan harin da aka kai a gidan yarin Kuje da ke Abuja a baya-bayan nan tare da tserewar fursunoni, Rundunar yan sandan Nasarawa ta ce ta kama wani Hassan Hassan, wanda sunansa da hotonsa ke cikin fursunoni da aka ce sun tsere cikin wadanda ake zargin yan Boko Garam ne a karamar hukumar Keffi.

Mai magana da yawun yan sandan Jihar Nasarawa, DSP Ramhan Nansel, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a Lafia, ranar Asabar, The Punch ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel