Shugaban kasa Buhari ya fadi abu 1 da zai bar wa ‘Ya ‘yansa gado idan ya bar Duniya

Shugaban kasa Buhari ya fadi abu 1 da zai bar wa ‘Ya ‘yansa gado idan ya bar Duniya

  • Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyarar gaisuwar sallah ga Sarkin Daura a mahaifarsa
  • Mai girma Muhammadu Buhari ya yi kira da babbar murya ga iyaye da matasa a kan tarbiya da ilmi
  • Buhari yake cewa sanin darajar ilmi ta sa bai bada auren ‘ya ‘yansa har sai sun yi Digirin farko tukuna

Katsina - Mai girma shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga iyaye da su tarbiyyantar da ‘ya ‘yansu da kyau, tare da nuna masu tsoron Ubangiji.

Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Laraba, 13 ga watan Yuli 2022, inda aka ji shugaban kasar yana wannan kira yayin da ya ziyarci fadar Sarkin Daura.

Shugaban kasar ya ziyarci fadar Mai martaba Umar Farouk Umar ne domin mika gaisuwar sallah. Hadiminsa, Garba Shehu ya bayyana haka a wani jawabi.

Kara karanta wannan

Tinubu ya birkita lissafin Gwamnonin Arewa da ya dauko Shettima – Hadimin Buhari

Da yake magana a garin na Daura da ke jihar Katsina, Muhammadu Buhari ya yi kira ga matasa su nemi ilmin zamani ba da nufin su samu aik a gwamnati ba.

Idan matasa suka samu sana’a da kwarewa ne za su iya kirkiro ayyukan yi, shugaban na Najeriya ya bada misali da kullen da aka yi a lokacin COVID-19.

Babu aiki a Gwamnatin Najeriya

Shugaba Buhari yake cewa a yanzu babu ayyukan yi a gwamnati, sai dai mutum ya nemi ilmin boko domin ya koyi sana’o’in zamani, kuma ya yaki talauci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban kasa Buhari
Shugaba Buhari a Lisbon Hoto: @GarShehu
Asali: Facebook

Har ila yau, Mai girma Buhari ya ce akwai bukatar a horas da manyan gobe ta hanyar samun ilmin yau da kullum da kuma fasaha ganin Duniya ta na canzawa.

Abin da Buhari ya fadawa 'Ya 'yansa

“An rufe ni na fiye da shekaru uku bayan na mulki kasar nan. A lokacin na fahimta, na fadawa ‘ya ‘yana darajarku na cikin kanku, ba abin da ku ka tara ba.”

Kara karanta wannan

Babban Lauyan Najeriya ya raba gardama game da takarar Musulmi da Musulmi a APC

“Kokari na shi ne horas da yaran wajen ganin za a iya damawa da su a duk inda suka samu kansu.”
“Na fadawa ‘ya ‘ya na, musamman mata, ba za su yi aure ba sai sun samu Digirin farko. Sun san babu abin da na bar masu a Duniya wanda za su ci gado."

- Muhammadu Buhari

An rahoto Garba Shehu ya na cewa Muhammadu Buhari ya ce babban abin da ya bar wa yaran da ya haifa a Duniya shi ne ganin cewa sun samu ilmi mai nagarta.

Siyasar 2023

Ku na da labari cewa a karon farko a cikin shekaru kusan 30, babbar jam’iyyar siyasa a Najeriya ta zabi ‘yan takararta na shugaban kasa duk su zama Musulmai.

Babatunde Ogala wanda Lauya ne wanda ya kai matsayin SAN a Najeriya, ya tsoma baki a kan takarar APC, ya ce yin hakan bai sabawa tsarin mulkin kasa ba.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Buhari ya fusata, ya yi kakkausan lafazi kan yajin aikin ASUU

Asali: Legit.ng

Online view pixel