Manyan Labarai A Yau
Bakaniken nan mai halin kirki da ya mayar da N10.8m da aka turo asusun ajiyar na banki a bisa kuskure ya bayyana ko naira nawa aka ba shi a matsayin tukwici.
Dakarun sojin saman Najeriya sun samu nasarar sheƙe mayaƙan ƙungiyar ta'addancin ISWAP tare da kwamandojinsu a wani farmaki da suka kai maɓoyarsu a jihar Borno.
Wani matashi ɗan Najeriya ya sanya hirar da suka yi da wata budurwa wacce ya so ya ce yana so a Twitter. A cikin hirar budurwar ta cika shi da jerin bukatu.
Wasu miyagun mahara sun halaka babban basaraken Fulani da ke a wani ƙauye a ƙaramar hukumar Zaria cikin jihar Kaduna. Maharan sun kuma halaka ƴaƴansa guda huɗu.
Shugabannin jam'iyyar PDP a jihar Imo sun ajiye muƙamansu tare da ficewa daga jam'iyyar gaba ɗaya. Sun ɗora alhakin hakan akan ɗan takarar gwamnan jam'iyyar.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙulla yarjejeniya da wasu ƙasashen nahiyar Afirika domin kawo ƙarshen mamaye kasuwar iskar gas ta Rasha a nahiyar Turai.
Hukumar DSS ta bankado wani shirin ƙulla-ƙulla da ake shiryawa kan gwamnatin tarayya da hukumar saboda cafke dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya, Emefiele
Ƴan sanda sun tabbatar da sun mayar da dukkanin motocin tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, da suka kwace gidajensa. Kotu ce ta umarci yin hakan.
Aƙalla mutum shida sun riga mu gidan gaskiya yayin da wasu da masu yawa suka jikkata a wani mummunan hatsarin mota da ya ritsa da fasinjoji 20 a jihar Oyo,
Manyan Labarai A Yau
Samu kari