Fitaccen Lauya Ya Yi Magana Kan Yiwuwar Tinubu Ya Kori Shugaban INEC Bayan Dakatar Da Bawa Da Emefiele

Fitaccen Lauya Ya Yi Magana Kan Yiwuwar Tinubu Ya Kori Shugaban INEC Bayan Dakatar Da Bawa Da Emefiele

  • Wani babban lauyan kare haƙƙin ɗan adam, Malcolm Omirhobo, ya bayar da dalilin da ya sanya shugaba Tinubu ba zai kori shugaban INEC ba
  • Omirhobo ya ce tsammanin shugaban ƙasar ya kori Mahmood Yakubu kamar jiran kaɗangare ne ya haifi kada
  • Lauyan ya yi iƙirarin cewa Shugaba Tinubu ya amfana da zamba da maguɗin da shugaban INEC ɗin yayi saboda haka ba zai iya korarsa ba

Jihar Legas - Wani fitaccen lauya a jihar Legas kuma ɗan rajin kare haƙƙin ɗan adam, Malcolm Omirhobo, a ranar Lahadi ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ba zai iya korar shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ba daga muƙaminsa.

Omirhobo shi ne lauyan nan da ya yi tashe a watan Yunin 2022, bayan ya je zaman kotun ƙoli sanye da shiga irin ta bokaye.

Kara karanta wannan

Jerin Mutum 12 Da Shugaba Tinubu Yakamata Ya Bincika Kan Wawure Dukiyar Kasa, Tsohon Dan Majalisa Ya Bayyana

Fitaccen lauya ya ce Tinubu ba zai iya korar shugaban INEC ba
Omirhobo ya ce Tinubu ba zai iya korar shugaban INEC ba Hoto: Malcolm Omirhobo, INEC Nigeria, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Fitaccen lauyan yana martani ne kan kiran da wani babban lauya kuma tsohon shugaban ƙungiyar lauyoyi ta ƙasa (NBA), Olisa Agbakoba, ya yi na a kori Farfesa Mahmood Yakubu daga muƙaminsa.

"Agbakoba ya yi kira mai wuyar aikatawa" A cewar Omirhobo

Tsohon shugaban na ƙungiyar lauyoyin ya bayyana cewa yakamata Yakubu ya sauka daga muƙaminsa saboda kada ya kawo tangarɗa kan ƙwasƙwarimar da ake yi wa fannin zaɓe a ƙasar nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A ganin Omirhobo, Shugaba Tinubu ba zai kori Farfesa Yakubu daga muƙaminsa ba saboda ya amfana da zamba da maguɗin da shugaban na INEC ya kitsa a zaɓen 2023.

Lauyan ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa:

"Kiran da Agbakoba ya yi ga Tinubu ya kori shugaban hukumar INEC abu ne mai wuyar aikatawa. Kamar tsammanin kadangare ne ya haifi kada."

Kara karanta wannan

Shin Dagaske EFCC Ta Gayyaci Tsohon Shugaban Kasa Kan Wawure Kuɗi? Gaskiya Ta Bayyana

"Ta yaya kake tsammanin wanda ya ci gajiyar zamba da maguɗin shugaban INEC ya kore shi? Abu ne wanda ba zai taɓa yiwuwa ba."

Shugaban INEC Zai Bayar Da Shaida a Kotu Kan Zaben Tinubu

A wani labarin, shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), Farfesa Mahmooɗ Yakubu, zai gurfana a gaban kotu domin bayae da shaida kan zaɓen Shugaba Tinubu.

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, shi ne ya gayyato shugaban na INEC domin bayar da shaida a gaban kotun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel