Hatsarin Mota Ya Ritsa Da Wasu Fasinjoji a Jihar Oyo, Akalla Mutum Shida Sun Rasu Yayin Da Dama Suka Jikkata

Hatsarin Mota Ya Ritsa Da Wasu Fasinjoji a Jihar Oyo, Akalla Mutum Shida Sun Rasu Yayin Da Dama Suka Jikkata

  • Aƙalla rayukan fasinjoji shida ne suka salwanta a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a jihar Oyo
  • Wasu mutane da dama daga cikin fasinjojin sun samu raunika daban-daban a mummunan hatsarin motan da ya auku
  • An alaƙanta dalilin aukuwar hatsarin da gudu wanda ya wuce ƙa'ida da lodin da ya fi ƙarfin motar da hatsarin ya auku da ita

Jihar Oyo - Aƙalla mutum shida sun riga mu gidan gaskiya yayin da wasu mutum 14 suka samu raunika, a wani hatsarin mota da ya auku a titin hanyar Ibadan-Oyo a ƙaramar hukumar Afijio ta jihar Oyo a ranar Asabar.

Shaidun gani da ido sun tabbatarwa da jaridar Punch cewa direban wata farar mota ƙirar Toyota Hummer mai cin fasinjoji 18 ce motar ta ƙwace masa.

Kara karanta wannan

Shin Dagaske EFCC Ta Gayyaci Tsohon Shugaban Kasa Kan Wawure Kuɗi? Gaskiya Ta Bayyana

Akalla rayuka shida sun salwanta a wani hatsarin mota a jihar Oyo
Akalla rayukan mutum shida sun salwanta Hoto: Punch.com
Asali: UGC

Tayar motar mai lamba Lagos JJJ 941 XA, ta fashe ne bayan ta taso daga fitacciyar kasuwar Akinyele a ƙaramar hukumar Akinyele.

An tattaro cewa fasinjojin cikin motar waɗanda dukkaninsu maza ne, suna tafiya ne zuwa yankin Arewacin Najeriya kafin aukuwar hatsarin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kwamandan hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa na yankin Atiba, Bayode Olugbesan, ya tabbatar da cewa mutum huɗu sun rasu kafin isar jami'ansu wajen, yayin da aka garzaya da sauran zuwa babban asibitin jihar Oyo.

Dalilin aukuwar hatsarin

Olugbesan, wanda ya ɗora alhakin hatsarin akan gudu wanda ya wuce ƙa'ida da cika lodi, ya tabbatar da cewa hatsarin ya ritsa ne da mutum 20. Ya ƙara da cewa an ajiye gawarwakin a ɗakin ajiyar gawa.

A kalamansa:

"Dukkanin waɗanda hatsarin ya ritsa da su maza ne inda za su tafi Arewacin Najeriya. Hatsarin ya auku ne a dalilin gudu wanda ya wuce ƙa'ida da cika lodi. Motar fasinjohi 14 yakamata ta ɗauki amma an cikota da fasinjoji 20."

Kara karanta wannan

Bayan Ganawa da Tinubu, Asri Dakubo Ya Tona Asirin Wasu Sojoji Da Ke Ɗaukar Nauyin Ɓarayin Mai a Najeriya

Kwamandan ya kuma yi kira ga direbobi da su riƙa kiyaye wa a yayin tuƙi, su daina gudu wanda ya wuce ƙa'ida, cika lodi da tafiyar dare.

Wata babbar ma'aikaciyar asibiti wacce ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana. cewa:

"Jami'an FRSC sun kawo mutum 15 (waɗanda suka samu raunika) zuwa asibitin, amma biyu daga cikinsu sun rasu bayan an yi musu taimakon gaggawa."

Mutum 18 Sun Halaka a Wani Mummunan Hatsarin Mota

A wani labarin na daban kuma, wasu fasinjoji da dama sun rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a jihar Kano.

Fasinjoji 18 ne suka rasa rayukansu inda wasu daga ciki suka ƙone ƙurmus a mummunan hatsarin mota.

Asali: Legit.ng

Online view pixel