Manyan Labarai A Yau
Bidiyon wani dan Najeriya yana tafiya kan kiret din kwai masu yawa ba tare da ko guda ya fashe ba ya bazu a intanet, wasu na mamaki har suna zargin asiri ne.
Abdulsamad Rabiu shugaban rukunin kamfanonin BUA, ya rasa sama da N1trn a cikin dukiyarsa. Hakan ya faru ne a dalilin faɗuwa ƙasa warwas da darajar naira ta yi.
Wata babbar kotu a jihar Kaduna ta yi fatali da ƙarar da tsohon gwamnan jihar Ƙaduna, Nasir Ahmed El-Rufai, ya shigar da Sanata Shehu Sani kan zargin ɓata suna.
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ƙara wa'adin shekarun ritayar ma'aikatan lafiya a jihar daga shekara 35 zuwa 40 suna aiki ko shekara 65 da haihuwa
Wani lakcara ɗan Najeriya ya koma roƙon ɗalibansa da su ke gida da su daure su dawo makaranta. Lakcaran ya gaya musu cewa karatu ya kankama su ƙoƙarta su dawo.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya shiga ganawa da tsohon shugaban ƙasa a mulkin soja, Abdulsalami Abubakar, a fadarsa da ke Villa a birnin tarayya Abuja.
Babban basaraken Agura na Gbagura, Oba Saburee Babajide Isola Bakre, Jamolu II, ya riga mu gidan gaskiya. Basaraken ya rasu ne a ranar Laraba 14 ga watan Yuni.
Babban sufeton ƴan sanda na ƙasa, Usman Baba Alkali, ya bayar da umarnin a kulle sakatariyoyin ƙananan hukumomin jihar Plateau saboda gudun ɓarkewar rikici.
Akwai manyan malaman addini musamman fastoci da suka zama gwamnoni a jihohinsu bayan sun shiga siyasa. Fastocin suna yin bankwana da coci su tsunduma siyasa.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari