"Wannan Bata Da Kunya": Hirar Wata Budurwa Da WanI Saurayi Ta Bar Baya Da Kura

"Wannan Bata Da Kunya": Hirar Wata Budurwa Da WanI Saurayi Ta Bar Baya Da Kura

  • Wata hira tsakanin wata budurwa ƴar Najeriya da wani saurayi wanda ta ke burgewa ta janyo cece-kuce a Twitter
  • Matashin ya shigar da buƙatarsa a wajen budurwar amma ita hankalinta ya fi karkata wajen cinye masa dukiya
  • Masu amfani da yanar gizo sun bayyana mabanbanta ra'ayoyi kan hirar wacce ta karaɗe shafin inda wasu suka yi ta caccakarta

Wata budurwa ƴar Najeriya ta sha suka sosai a yanar gizo bayan hirar da ta yi a Twitter da wani matashi da ya nuna yana ra'ayinta ta bayyana.

Matashin ya yi mata magana ta DM domin gaya mata cewa yana ra'ayinta sannan ya buƙaci da ta ba shi lambar waya.

Matashi ya fitar da hirarsu da wata budurwa
Matashi ya bayyana hirarsu da budurwar da ta nemi ya siya mata Hollandia Hoto: Chad Henning/ Getty images, drayy09/ Twitter.
Asali: UGC

Sai dai, budurwar a cikin amsar da ta ba shi, ta buƙaci sai ya nemi cancantar samun lambarta ta hanyar siyo mata shawarwa da abin sha mai suna Don Simon.

Kara karanta wannan

DSS Ta Bankado Wata Kulla-Kulla Da Ake Shiryawa Gwamnatin Tarayya Kan Tsare Emefiele, Bayanai Sun Fito

Ta kuma ci gaba da buƙatar sai ya siyo wa ƙawarta Hollandia yoghurt duk lokacin da suka amince cewa za su fita yawon hira.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hirar ta su dai ta tayar da ƙura a yanar gizo, inda mutane da dama musamman maza suka caccaketa bisa wannan buƙatu da ta zayyano.

A yayin da yake sanya hirar ta su, matashin wanda ya fusata ya kira budurwar da 'mara kunya.'

Masu amfani da yanar gizo sun yi martani bayan budurwa ta nemi wasu abubuwa a hannun saurayi

Big Ayo ya rubuta:

"Allah mai iko. Ƙanwarta kuma fa da maƙwabta.?

Khaleed ya rubuta:

"Ina karantawa ina jin ƙyama."

Obideyi Emmy ya rubuta:

"Wannan tabbas rashin kunya ne."

Day Von ya rubuta:

"Maganar gaskiya wasu ƴan matan mayunwata ne! Kamata ya yi kawai su ɗauki kwano a gidajensu su je bakin titi a yi abinda aka saba."

Kara karanta wannan

"Har Lakada Min Duka Ta Taba Yi": Magidanci Ya Garzaya Kotu Neman a Korar Masa Tsohuwar Matarsa Daga Gida

Kyakkyawar Budurwa Ta Koka Kan Rashin Samun Saurayi

A wani labarin, wata kyakkyawar budurwa ƴar Najeriya mai rayuwa a ƙasar waje ta koka kan yadda samari basa kulata a can ƙasar da ta ke rayuwa.

Budurwar ta bayyana cewa duk da ƙwalliyarta da kyawun da ta ke da shi, idan ta fito waje babu mai taya wa. Hakan ya sanya tace za ta tattaro ta dawo gida Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng