Shugabannin Jam'iyyar PDP Sun Yi Murabus Tare Da Ficewa Daga Jam'iyyar, Sun Bayyana Dalilansu

Shugabannin Jam'iyyar PDP Sun Yi Murabus Tare Da Ficewa Daga Jam'iyyar, Sun Bayyana Dalilansu

  • Shugabannin jam'iyyar PDP a jihar Imo, sun yi murabus daga muƙamin shugabancinsu na jam'iyyar a jihar ranar Lahadi
  • Collins Opuozor, kakakin jam'iyyar a jihar tare da wasu shugabannin sune suka sanar da matsayarsu a wani taron manema labarai ranar Lahadi
  • Fusatattun shugabannin sun yi zargin cewa ɗan takarar gwamnan jihar na jam'iyyar, Samuel Anyanwu, yana farautar rayukansu

Owerri, Imo - Shugabannin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) guda bakwai a jihar Imo sun yi murabus daga muƙamansu na shugabancin jam'iyyar a jihar.

Collins Opuozor, kakakin jam'iyyar a jihar tare da sauran shugabannin su ne suka sanar da hakan ga ƴan jarida a ranar Lahadi, 18 ga watan Yuni, a birnin Owerri yayin da su ke sanar da yin murabus daga jam'iyyar, rahoton Vanguard ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Sabuwar Rigima Ta Sake Kunno Wa a Tsakanin Wike Da Atiku a Jam'iyyar PDP

Shugabannin PDP a jihar Imo sun yi murabus
Shugabannin sun ce Anyanwu na farautar rayuwarsu Hoto: @SenSamAnyanwu
Asali: Twitter

Shugabannin PDP a jihar Imo sun bayyana dalilin da ya sanya suka yi murabus

Fusatattun shugabannin jam'iyyar sun yi zargin cewa ɗan takarar jam'iyyar a zaɓen gwamnan jihar na watan nuwmaba, Samuel Anyanwu, yana bibiyarsu da rikici da barazana tare da ƙoƙarin cutar da su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugabannin sun kuma bayyana cewa ɗan takarar gwamnan ba ya da ƙwarewa da gogewar da zai mulki jihar Imo, cewar rahoton The Punch.

Shugabannin basu bayyana jam'iyyar da za su koma ba bayan ficewarsu daga jam'iyyar ta PDP.

Anyanwu shi ne ɗan takarar gwamnan jam'iyyar PDP a jihar a zaɓen da ke tafe inda tuni har hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta sanya sunansa cikin jerin ƴan takara.

Ɗan takarar na jam'iyyar PDP zai fafata ne da ɗan takarar gwamnan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) kuma gwamnan jihar mai ci yanzu, Hope Uzodinma wanda yake fatan koma wa kan kujerar karo na biyu.

Kara karanta wannan

Cikakken Jerin Gwamnonin APC, PDP Da Suka Halarci Zaben Shugabannin Majalisa Ta 10

Sabuwar Rigima a PDP Tsakanin Wike Da Atiku

A wani labarin, tsugunne bata ƙare ba a jam'iyyar adawa ta PDP, bayan wata sabuwar wutar rikici ta kunnon tsakanin tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike da Atiku Abubakar.

Rigimar ta samo asali ne kan kujerar shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa wanda Wike da Atiku kowa yake da ɗan takarar da yake goyon baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel