Manyan Labarai A Yau
Allah ya yi wa Yariman Gombe, mai martaba Alhaji Abdulkadir Abubakar Umar, rasuwa. Marigayin ya rasu ne bayan ya daɗe yana fama da jinya, na tsawon lokaci.
Miyagun ƴan bindiga sun halaka bayin Allah tare da sace wasu masu yawa a jihar Zamfara a wani mummunan hari da suka kai. Jihar ta daɗe da matsalar ƴan bindiga.
Wata gobara ta tashi a wasu shagunan dake cikin babbar kasuwar birnin Yola na jihar Adamawa. Gobarar ta laƙume kayayyaki na masu yawa a shagunan da ta tashi.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya samu sabon gargaɗi na kada ya yi amfani da ƙarfin soja akan sojojin da suka kifar da gwamnatin farar hula a Jamhuriyar Nijar.
Ƙungiyar ƙwadago ta musanta batun cewa ta dakatar da zanga-zangar da ta shirya gudanarwa a sakamakon tsige tallafin man fetur da gwamnatin Shugaba Tinubu ya yi.
Gwamnan jihar Borno ya shirya tallafawa mabuƙata sama da mutum 1.8m a jihar Borno. Gwamnan ya ƙaddamar da sabon rabon tallafi wanda mabuƙata 1.8m za su amfana.
Wani jirgin sama mai saukar ungulu ya yi hatsari a jihar Legas. Jirgin saman ya fado ne kan gine-gine a birnin na Legas a kusa da tashar jirgin sama ta Murtala.
Kungiyar dillalan man fetur (IPMAN) ta koka kan yadda cire tallafin man fetur ya tilasta da yawa daga cikin mambobinta haƙura da sana'ar saboda rashin riba.
Majalisar dattawa za ta kammala tantance ministocin da Shugaba Tinubu ya naɗa a yau Talata. Majalisar za ta tantance ragowar ministocin su 14 a yau Talata.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari