Manyan Labarai A Yau
Ƴan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun kai farmaki a gidan tsohon ministan watsa labarai, Labaran Maku cikin gidansa a jihar Nasarawa.
Miyagun ƴan bindiga sun kai wani mummunan sumame cikin tsakar dare a wasu ƙauyukan jihar Bauchi, inda suka halaka mutum biyu da sace wasu mutum biyu daban.
Jam'iyyar Action Alliance (AA), ta gabatar da buƙatunta a gaban kotun zaɓen inda ta nemi kotun da ta ƙwace nasarar da mataimakin kakakin majalisar wakilai.
Gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno ya bayyana dalilan da ya sanya ya sake naɗa kwamishinonin da suka yi aiki a gwamnatin magabacinsa, tsohon gwamna Udom Emmanuel.
Rayukan mutum shida ne suka bar duniya bayan sun kwankwaɗi barasa a jihar Ogun. Mutanen dai sun ce ga garin ku nan ne bayan shan barasar wacce abokinsu ya basu.
Kungiyar ɗalibai ta ƙasa (NANS) ta shirya gudanar da zanga-zangar bai ɗaya kan ƙarin kuɗin makarantu da aka yi a makarantun gaba da sakandire a faɗin ƙasa nan.
Wasu ƙananan yara guda biyu sun riga mu gidan gaskiya a jihar Legas bayan katanga ta rufto akan gidansu a dalilin ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka yi.
Tsohuwar kwamishiniya a ma'aikatar harkokin mata ta jihar Kano, Barr. Zubaida Damakka Abubakar, ta rasu. Marigayiyar ta rasu bayan ƴar gajeruwar jinya a Abuja.
Wata ma'aikaciyar otal ta yi abin a yaba bayan ta dawo da $70,000 da ta tsinta a otal ɗin da take aiki. Budurwar mai suna Ngozi ta mayar da kuɗin gaba ɗaya.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari