An Samu Asarar Dukiya Yayin Da Gobara Ta Lalata Shaguna 14 a Babbar Kasuwar Jihar Adamawa

An Samu Asarar Dukiya Yayin Da Gobara Ta Lalata Shaguna 14 a Babbar Kasuwar Jihar Adamawa

  • Wata mummunar gobara da ta tashi a babbar kasuwar birnin Yola na jihar Adamawa ta laƙume shaguna 14
  • Gobarar ta tashi ne a dalilin fashewar wani tulun gas inda ta lalata dukiya mai tarin yawa a shagunan
  • Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya ziyarci kasuwar inda ya bayar da tallafin N5m ga ƴan kasuwar da gobarar ta shafa

Jihar Adamawa - Aƙalla shaguna 14 na hatsi, kayan abinci da sauran wasu kayayyaki suka lalace a dalilin wata gobara wacce ta auku da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar ranar Talata, a babbar kasuwar Yola a jihar Adamawa.

Darektan hukumar kashe gobara ta jihar Adamawa, Mr Abdullahi Adamu, ya bayyana cewa an kashe gobarar ne ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin jami'an hukumar kashe gobara ta jihar da na hukumar kashe gobara ta tarayya, cewar rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Sabon Gwamna Zai Raba Buhuna 36, 000 na Kayan Abinci Kyauta a Kowane Gari

Gobara ta lakume shaguna a birnin Yola
Hoton wajen wata gobara (ba inda lamarin ya auku ba) Hoto: Tribuneonline.com
Asali: UGC

Sauran da suka taimaka wajen kashe gobarar sun haɗa da ma'aikakan jami'ar AUN da kamfanin ruwa na Faro.

Ya bayyana cewa dokar kullen da aka sanya a jihar, ta taimakawa jami'an kashe gobarar shawo kan matsalar cikin sauƙi, ba tare da ɓata-gari sun kwashe kayayyakin da aka ciro daga cikin shagunan ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adamu, ya yi nuni da cewa gobarar ta tashi ne a dalilin fashewar wani tulun gas a wajen wani cin abinci a kasuwar, sannan ta ruru a dalilin kwararar mai daga jikin wani injin janareto na wani gidan abinci dake kusa da wajen.

A kalamansa:

"Babu wanda ya rasu a gobarar. A halin yanzu ba za a iya ƙiyasta kuɗin asarar kayayyakin da aka yi ba."
"Hukumar kashe gobara ta jiha za ta duba wajen da lamarin ya auku domin gano yawan asarar da aka tafka."

Kara karanta wannan

Rikici Yayin Da Wata Mai Koyon Sana’a Ta Tsere Da Jinjirin Uwar Dakinta Dan Kimanin Watanni 2 A Wurin Biki, An Bazama Nemanta

"Jami'an kashe gobarar na isa wajen da lamarin ya auku, suka duƙufa kashe gobarar inda suka samu nasarar kashe ta cikin sa'a ɗaya."

Gwamna Fintiri ya ba ƴan kasuwar tallafi

Gwamna Ahmadu Fintiri, ya ziyarci kasuwar inda ya bayar da tallafin N5m, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Gwamnan wanda ya ziyarc shaguna 10 da gobarar ta fi lalatawa, ya bayyana cewa kowane mai shago cikin shaguna 10 da suka fi lalacewa zai samu tallafin N500,000 domin sake siyo kaya su ci gaba da kasuwancinsu.

Gobara Ta Lakume Shaguna a Jihar Kwara

A wani labarin kuma, wata mummunar gobara ta laƙume rukunin wasu shaguna a birnin Ilorin na jihar Kwara.

Gobarar wacce ta tashi a dalilin tartsatsin wutar lantarki ta laƙume kadarori na miliyoyin naira.

Asali: Legit.ng

Online view pixel