Yan Bindiga Sun Sace Mutum 13 a Wani Sabon Hari a Jihar Zamfara

Yan Bindiga Sun Sace Mutum 13 a Wani Sabon Hari a Jihar Zamfara

  • Ƴan bindiga sun kai sabon harin ta'addanci a ƙauyen Mayanchi dake ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara a yankin Arewa maso Gabas na Najeriya
  • Miyagun ƴan bindigan sun halaka mutum uku tare da sace wasu mutum 13 a harin da suka kai a ƙauyen na Mayanchi
  • Jihar Zamfara ta daɗe tana fama da matsalar rashin tsaro wacce ƴan bindiga suka haifar inda su ke cin karensu babu babbaka

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Zamfara - Ƴan bindiga sun halaka mutum uku da sace wasu mutum 13 a wani hari da suka kai a ƙauyen Mayanchi cikin ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara.

Harin da ƴan bindigan suka kai a ranar Litinin a ƙauyen na zuwa ne ƴan kwanaki bayan an sace mata 23 da wasu ma'aikata a ƙananan hukumomin Maradun da Talata Mafara.

Kara karanta wannan

Tsadar Mai: IPMAN Ta Koka, Ta Bayyana Yadda 'Yan Kasuwar Man Fetur Ke Ji a Jika a Dalilin Cire Tallafi

Yan bindiga sun kai sabon hari a Zamfara
Yan bindigan sun halaka mutum biyu a yayin harin Hoto: Channelstv.com
Asali: UGC

Wani mazaunin ƙauyen mai suna Aminu Mayanchi, ya gayawa jaridar Daily Trust cewa ƴan bindigan sun farmaki ƙauyen ne da misalin ƙarfe 11:00 na safe inda suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi.

Ƴan bindigan sun kutsa cikin masallaci sun tasa ƙeyar bayin Allah

Aminu ya bayyana cewa daga baya ƴan bindigan sun je gidan wani marigayi Ibrahim Mayanchi wanda ya taɓa rike ma'ajin ƙungiyar ƴan jarida ta ƙasa (NUJ) a Zamfara, inda suka yi awon gaba da ƴaƴansa gudu uku.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Sun harbe mutum ɗaya bayan ya ƙi yarda su tafi da shi. Daga baya sai suka shiga wani masallaci inda wasu mutane ciki har da shugaban ƴan sakai na ƙauyen suka ɓoye, sannan suka tasa ƙeyarsu." A cewarsa.

Daga cikin waɗanda ƴan bindigan suka halaka har da tsohon shugaban jam'iyyar APC na mazaɓar Mayanchi, Dahiru Maizabura, rahoton Premium Times ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu Zai Gabatar Da Jawabi Ga 'Yan Najeriya, Bayanai Sun Fito

Ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Zamfara ba, ASP Yazid Abubakar, saboda layukan wayarsa a kashe su ke.

Matsalar ƴan bindiga ta daɗe tana ci wa al'ummar jihar Zamfara tuwo a ƙwarya, inda rayukan mutane da dama suka salwanta da rasa matsugunansu da dukiyoyinsu.

'Yan Bindiga Sun Halaka Masu Kai Kudin Fansa

A wani labarin kuma, tsautsayi ya faɗa kan wasu masu kai kuɗin fansa bayan da ƴan bindiga suka halaka su a jihar Plateau.

Mutanen guda biyu waɗanda matasa ne sun je kai kuɗin fansar ne domin ceto ƴan uwansu da ƴan bindigan suka yi awon gaba da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel